Skip to main content

Posts

UMMDATUL AHKAM: BABIN BAYANIN JININ HAILA

UMDATUL AHKAM باب الحيـــض: 40- عن عائشة رضي الله عنها "أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سألت النبي صلى الله عليه وسلم، فَقَالت: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فقالَ: لاَ، إِنَّ ذَلِكَ دَمُ عِرْقٍ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ اْلأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلَّى". وفي رواية: "وَلَيْسَتْ بِالْحَيْضَةِ، فَإِذَا أَقْبَلَتِ الْحَيْضَةُ فَاتْرُكِي الصَّلاَةَ فِيهَا، فَإِذَا ذَهَبَ قَدْرُهَا فَاغْسِلِي عَنْكِ الدَّمَ وَصَلِّي". BABUN DA ZAI YI BAYANI A GAME DA HUKUNCIN JININ HAILA: 40- An karvo daga (Nana) Aishatu (R.A) tace haqiqa Faximatu xiyar Abi Hubaishin ta tambayi annabin Allah (S.A.W.) sai tace (da shi): (Ya ma'aikin Allah) ni mace ce da nake yawan zubar jinin haila bani da tsarki shin ko na bar yin sallah? Sai ma'aiki (S.A.W.) yace da ita a'a, (ai ba kya bari ba) domin ai shi wannan wani jinin da yake zubowane daga wata jijiya (dake jikin mahaifa), sai dai ke abin da ya wajaba kiy...

MAGANIN KARYA ASIRI KO JIFA

Ga Mata masu lalurar fitar ruwa masu Kaikayi daga Farjin su.  A gwada daya daga cikin wadannan:- 1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi. 2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. . 3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection. . 4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba. 5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rash...

Maganin Yawan Fitar Ruwa Mai Kai-kayj Afarjji

Ga Mata masu lalurar fitar ruwa masu Kaikayi daga Farjin su.  A gwada daya daga cikin wadannan:- 1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi. 2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. . 3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection. . 4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba. 5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rash...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

Yadda zak Goge ko Dakatar Da Facebook Ɗinka

Yadda za a goge asusun Facebook na dindindin a cikin matakai 3 masu sauƙi James Laird | Dalian da suke Mutun tunanon share facebook account ɗinsa Sune kamar haka:- Ko dai kana damuwa da wasu sirri kanka ta yanar gizo, ko kuma kawai kana gajiya da sabuntar shigar yau da kullun daga abokai na Mu'amula, ko abokai na makaranta, waɗanda ka fahimci cewa a zahiri basu da kyaky-kyawan hali, akwai wasu dalilan da yawa, da yasa zaka so ka share asusun Facebook din ka - kuma yin hakan ba shi da wahala In sha Allahu, ba kamar yadda mitane suke tunani ba. A cikin wannan maƙalar, zamuyi bayanin yadda zaka share Facebook-mataki-mataki, gami da bayyana bambanci tsakanin 'Dakatar da asusun', da kuma goge shi gaba daya. Idan kana tunanin share asusunka to ba kai bane farau. Hakan na faruwane sakamakon ɓacin rai game da tasirin matsalolin kafofin watsa labarun da ke shafar lafiyar mutum da rayuwarmu, da yawa mutane sukan ci gaba da juya baya ga waɗannan rukunin yanar gizon da suk...

YADDA AKE WANKAN GAWA

TUNATARWA WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA FALALAR WANKAN GAWA Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’ A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace: ”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin). SHARUDDAN WANKAN GAWA: Daga cikin sharaddan wankan gawa sune: {1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali: Iyaye. kanne ko yayyek “ya”yansa da sauransu). {2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta). {3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi. YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali: Sau Uku (3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9). Hakan ya tabbata daga Manzon Al...

ƘUNGIYAR MANOMA TAYI MAGANA

MANOMA: DAGA YANZU BUHUN SHINKAFA BA ZAIWUCE 15,000 BA. By: Muhammadu Auwal Umar A korarin karfafa wa gwamnatin tarayya na hana fasakaurin shinkafa a kasar nan, kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya ta ce, daga yanzu buhun shinkafa ba zai wuce naira 15,000 ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamin a garin Abuja, shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIPAN), Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya. Ya kara da cewa, shinkafar gida da ake yi a Nijeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000. Kungiyar ta bayyana cewa, ta rubuta wa gwamnatin tarayya wasika wajen karya farashin shinkafa, domin ta karfafa wa gwamnati wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan. Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Nijeriya tana asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin. Alhaji Moha...

Tsarin Fasahar Fai fai DVD (1)

TSARIN FASAHAR FAI FAIFAN DVD (1) A kashi na uku mai karatu ya ci karo ne da bayanai dalla-dalla kan kimiyya da fasahar da suke qunshe cikin faifan CD, da falle-falle da aka sarqafe wuri xaya don inganta tsarin zubawa da sarrafa bayanai cikin sauki. Ahalin yanzu za mu ci gaba, inda za mu tavo fasaha ta gaba, wato: Faifan DVD. Matashiya Makonni uku da suka gabata muka fara gabatar da bayanai tiryan-tiryan kan tsarin ma’adanar bayanai, daga na dauri zuwa waxanda muke amfani dasu a wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa. A babin matashiya, mun gabatar da bayani kan hanyoyin da xan adam ya biyo a baya wajen taskance bayanai a tsarin da ya samu kansa a ciki; da irin ci gaban da ya samu daga baya – daga haddace abubuwa zuwa rubutu da karatu. Mai karatu ya qara ji har wa yau, sadda xan adam ya fara dogaro da ci gaban qere-qere wajen adana bayanansa. Kashi na biyu ya leqa xakin tarihi ne, inda na naqalto mana tarihi da asalin faifan tangaraho, da faifan CD, wanda a harshen tura...

Hukunci Wanda Yayi Zina Da Wadda Ba Musulmaba

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA. Hukuncinka daidai yake da na kowanne mazinaci. Da farko dai kaci amanar kanka Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi. Sannan kaci amanar hukumar Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al ummar wani yankin da ba naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin. Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari ar musulunci?. Kaima kasan bashi da hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku dakai dashi. Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin muminan kirki awajen Allah. Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen Allah, yana ha data waje guda ne tare da shirka da kisan kai. Sune laifuka uku mafiya girma a Musulunci. Allah yana magana acikin Alqur ani game da siffar bayinsa na kwarai, yace : SUNE WADANDA BASU KIRAN WANI ABIN BAUTA TAR...

Kayan Aikin Gina Manhajar Kwamfuta Kashi na1

Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta (1) A Kashi na bakwai cikin binciken da muke yi kan tsarin gina manhajar kwamfuta. A sha karatu lafiya. Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta Kafin aiwatar da kowane irin aiki, Magina manhajar kwamfuta na bukatar kayan aiki. Wadannan kayayyakin aiki suna da yawa, dangane da girma ko mahimmancin manhajar da ake son ginawa. A tare da haka, akwai wadanda suke wajibi ne, akwai kuma wadanda samuwarsu abin so ne, ba wajibi ba. Ga wasu daga cikin kayayyakin aikinsu nan: Ilimi da Kwarewa: Wannan shi ne abu na farko. Magina manhajar kwamfuta kwararru ne, wadanda suka san kan kwamfuta da rayuwarta, da lafiyarta, da makisanta. Sanayya a wannan mahanga abin so ne wajen gina manhajar kwamfuta. Wannan ilimi kuwa ya hada da kwarewa a fagen dabarun gina manhajar da ake son amfani da shi. Ba dole bane sai ka san dukkan dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages), a a. Misali, kana iya gina manhajar kwamfuta da na wayar salula ta amfani da...

Mu'ujizar Alqu'ani Mai Girma

Gaskiyar Yadda Akeyin Ruqiya, A Musulinci Gaskiyar yadda akeyin Ruqiya, A Musulunci Watch and Understand youtube HD

New Video

youtube HD

Addu'o'i Managarta Masu Albarka

Adu'o'i Masu Fa'ida Da Albarka, من الكتاب الحسن المسلم Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Fita Daga Bandaki. غُفْرَانَكَ. Ghufranak. Ya Allah! Gafararka (na ke nema) Zikiri yayin fara Alwala. بِسْمِ اللهِ. Bismi l-lahi Zikiri Bayan Gama Alwala أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ. Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; k...

Halifofin Shehu Ibrahim Inyass Na Nigeria

Halifofin Shehu Ibrahim Inyanss Halifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannunsa ✍️ Rayyahi Sani Khalifa Akwai wasu daga cikin halifofin Shehu a Najeriya wadanda Allah yayi musu baiwa da samun mukadamanci kai tsaye daga hannun Shehu RA, kamar yanda na samu a cikin littafin ( رجال وادوار حول صاحب الفيضة ) wanda Sheikh Muhammad dan Shehu Abdullahi Altijani ya rubuta. A cikin wannan littafin mawallafin ya tattara sunaye da takaitattun bayanai akan kowani Shehi, da kuma ainihin wasiqar/shahadar da Shehu ya rubutawa kowanni daya daga cikinsu na mukaddamanci. Wadannan shehunnai su ke da izini mudlaqi na bada darika da mukadamanci da bada izinin karanta asraran tijjaniyya ga wanda suka ga dama a kuma lokacin da suka ga dama daga wajen Shehu RTA. Wadannan dai sune tushen Faidha a Najeriya dan haka muridai da sauran al'umma ku sani cewa duk wani abu da ake danganta shi da faidha idan bai fito daga wadannan zawiyoyin ba ko rasan da su...

Yadda Zaka Samu Space A wayarka, Bayan Tacika

YADDA ZAKA SAMU 'MORE SPACE' AWAYARKA TA ANDROID, BAYAN TA CUSHE Assalamu Alaikum yaa Ƴan uwana Maza da Mata ma'abota bibiyarmu awannan Shafi mai Albarka. A yau made, da ikon Allah mun zomuku da wata tsarabar wadda zata amfane ku wajen magance matsalar da take addabar ku Awayoyinku, na ƙaraci Space. Yayi dai dai ASHA KARATU LAFIYA..... Kamar yadda kuka sanine sau da yawa mutun zaga bashi da wani Abu (files, images, apps, videos, music, e.t.c) da yawa akan wayarka amma kanaso ka Sauko da wani abu ko Atura maka, kawai sai wayar tace maka (is not enough space delet some), to In sha Allahu nesa tazo kusa. Kawai matakin farko da zakabi har ƙarshe shine:- 1. Ka shiga menu na wayarka. 2. Sai file manager 3. Danna internal memory 4. Shiga Home 5. Zaɓi ko shiga memory na kan Wayar 6. Ka duba duk folders da kake da su 7. Wanda kaga akwai wani abu mai amfani, sai ka bar shi, ko kuma ka Select (zaɓi), sai ka dubu duk inda kaga ansa alamar Almakashi, saika taɓa shi, koda g...

Ganduje Da Mataimakan Gwamnoni Uku Sun Tsalake Rijiya Da Baya

An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna legit.ng Jul 29, 2019 5:49 AM Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya ga ta kansa yayin da rikici ya kaure a filin wasan kwallon kafa ta Ahmadu Bello dake garin Kaduna, ABS, inda har sai da Yansanda suka dinga harba barkonon tsohuwa a cikin jama’a. Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli bayan an kammala wasan karshe na gasar AITEO Cup tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes. Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasan ya kai ga bugun daga kai sai gola sakamakon kunnen doki da aka tashi, daga karshe Kano Pillars ta samu nasara da ci 4-3, sai dai magoya bayan Pillars sun shiga fili a guje don murna, inda jami’an tsaro suka taresu, daga nan fa sai rikici ya kaure, shine dalilin da yasa Yansanda suka shiga harba barkonon tsohuwa. Daga cikin wadanda rikicin ya rutsa dasu akwai gwamnan jahar Kano da ya je goy aba Pilla...

Falalar Goma Farko Na Zul-Hajji

*Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji* An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: Ranar Daya Ga Watan zilhijja ita ce Ranar Da Allah (swt) ya Gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk Wanda Ya Azimci Wannan Rana Allah(SWT) zai Gafarta Masa kowane irin zunubi tsakaninsa da shi. (2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan Rana yana da lada kwatankwacin wanda ya Raya shekara da ibada . (3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan Rana Allah (SWT) zai karbi Adduo’insa. (4) Ranar Hudu Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya Azimci wannan Rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu. (5) Ranar Biyar Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya Azimci Wannan Rana Allah (SWT) zai kare shi daga munafunci ko azab...