Meye “Ethical Hacking” Kuma? Daga Taskar Baban Sadik Kalmar “Hacking” dai kamar yadda mun sha bayanai a kai, shi ne amfani da kwarewa a fannin na’urori da hanyoyin sadarwa, don isa ga bayanai dake wata na’ura, wanda a al’adance ba kowa ke iya isa gare su ba. Ko amfani da kwarewa wajen iya sarrafawa da kuma mallake na’urori da hanyoyin sadarwa cikin sauki. Idan aka ce: “Hack” a turancin sadarwa na zamani, yana iya daukan ma’anar amfani da kokari na musamman wajen ganin “kwakwaf,” kan yadda wata na’ura ko wata hanya ta sadarwa ke aiki. Wannan halattacciyar ma’anar wannan kalma kenan. To amma da tafiya tayi nisa, sai ma’anarta a kwakwalen mutane ta canza, saboda samuwar masu amfani da wannan kwarewa wajen aiwatar da ta’addanci ga kwamfutoci ko na’urorinsu, ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani. Wannan yasa da zarar ka ji ance “Hacker” ko “Hacking,” nan take ba abin da zuciyarka za ta hararo maka sai aikin ta’addanci ta hanyar sadarwa, ko wani dan ta’adda a fagen sadarwa na zamani;
An ƙirƙiri wannan shafine don ilimintarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa, wa'azantarwa akan Al'amuran "sadarwa"