Skip to main content

Posts

Showing posts from August, 2019

YADDA AKE WANKAN GAWA

TUNATARWA WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA FALALAR WANKAN GAWA Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’ A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace: ”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin). SHARUDDAN WANKAN GAWA: Daga cikin sharaddan wankan gawa sune: {1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali: Iyaye. kanne ko yayyek “ya”yansa da sauransu). {2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta). {3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi. YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali: Sau Uku (3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9). Hakan ya tabbata daga Manzon Al

ƘUNGIYAR MANOMA TAYI MAGANA

MANOMA: DAGA YANZU BUHUN SHINKAFA BA ZAIWUCE 15,000 BA. By: Muhammadu Auwal Umar A korarin karfafa wa gwamnatin tarayya na hana fasakaurin shinkafa a kasar nan, kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya ta ce, daga yanzu buhun shinkafa ba zai wuce naira 15,000 ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamin a garin Abuja, shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIPAN), Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya. Ya kara da cewa, shinkafar gida da ake yi a Nijeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000. Kungiyar ta bayyana cewa, ta rubuta wa gwamnatin tarayya wasika wajen karya farashin shinkafa, domin ta karfafa wa gwamnati wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan. Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Nijeriya tana asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin. Alhaji Moha

Tsarin Fasahar Fai fai DVD (1)

TSARIN FASAHAR FAI FAIFAN DVD (1) A kashi na uku mai karatu ya ci karo ne da bayanai dalla-dalla kan kimiyya da fasahar da suke qunshe cikin faifan CD, da falle-falle da aka sarqafe wuri xaya don inganta tsarin zubawa da sarrafa bayanai cikin sauki. Ahalin yanzu za mu ci gaba, inda za mu tavo fasaha ta gaba, wato: Faifan DVD. Matashiya Makonni uku da suka gabata muka fara gabatar da bayanai tiryan-tiryan kan tsarin ma’adanar bayanai, daga na dauri zuwa waxanda muke amfani dasu a wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa. A babin matashiya, mun gabatar da bayani kan hanyoyin da xan adam ya biyo a baya wajen taskance bayanai a tsarin da ya samu kansa a ciki; da irin ci gaban da ya samu daga baya – daga haddace abubuwa zuwa rubutu da karatu. Mai karatu ya qara ji har wa yau, sadda xan adam ya fara dogaro da ci gaban qere-qere wajen adana bayanansa. Kashi na biyu ya leqa xakin tarihi ne, inda na naqalto mana tarihi da asalin faifan tangaraho, da faifan CD, wanda a harshen tura

Hukunci Wanda Yayi Zina Da Wadda Ba Musulmaba

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA. Hukuncinka daidai yake da na kowanne mazinaci. Da farko dai kaci amanar kanka Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi. Sannan kaci amanar hukumar Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al ummar wani yankin da ba naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin. Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari ar musulunci?. Kaima kasan bashi da hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku dakai dashi. Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin muminan kirki awajen Allah. Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen Allah, yana ha data waje guda ne tare da shirka da kisan kai. Sune laifuka uku mafiya girma a Musulunci. Allah yana magana acikin Alqur ani game da siffar bayinsa na kwarai, yace : SUNE WADANDA BASU KIRAN WANI ABIN BAUTA TAR

Kayan Aikin Gina Manhajar Kwamfuta Kashi na1

Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta (1) A Kashi na bakwai cikin binciken da muke yi kan tsarin gina manhajar kwamfuta. A sha karatu lafiya. Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta Kafin aiwatar da kowane irin aiki, Magina manhajar kwamfuta na bukatar kayan aiki. Wadannan kayayyakin aiki suna da yawa, dangane da girma ko mahimmancin manhajar da ake son ginawa. A tare da haka, akwai wadanda suke wajibi ne, akwai kuma wadanda samuwarsu abin so ne, ba wajibi ba. Ga wasu daga cikin kayayyakin aikinsu nan: Ilimi da Kwarewa: Wannan shi ne abu na farko. Magina manhajar kwamfuta kwararru ne, wadanda suka san kan kwamfuta da rayuwarta, da lafiyarta, da makisanta. Sanayya a wannan mahanga abin so ne wajen gina manhajar kwamfuta. Wannan ilimi kuwa ya hada da kwarewa a fagen dabarun gina manhajar da ake son amfani da shi. Ba dole bane sai ka san dukkan dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages), a a. Misali, kana iya gina manhajar kwamfuta da na wayar salula ta amfani da

Mu'ujizar Alqu'ani Mai Girma

Gaskiyar Yadda Akeyin Ruqiya, A Musulinci Gaskiyar yadda akeyin Ruqiya, A Musulunci Watch and Understand youtube HD

New Video

youtube HD

Addu'o'i Managarta Masu Albarka

Adu'o'i Masu Fa'ida Da Albarka, من الكتاب الحسن المسلم Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Fita Daga Bandaki. غُفْرَانَكَ. Ghufranak. Ya Allah! Gafararka (na ke nema) Zikiri yayin fara Alwala. بِسْمِ اللهِ. Bismi l-lahi Zikiri Bayan Gama Alwala أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ. Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; k