Skip to main content

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER...

Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani,

Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka.

Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan.

Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin sabon PIN dinka kawai saika rubuta 0000 1234 1234 saika aika zuwa 777 nan take zaayoma sako cewa Your PIN is been change, wannan shine idan da tambaya ko neman karin bayani kofa a bude take kayi rijista saika rubuta tambayarka a anan kasa dan wadanda sukayi rijistane kawai zasu iya rubutu anan.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...