Skip to main content

UMMDATUL AHKAM: BABIN BAYANIN JININ HAILA

UMDATUL AHKAM
باب الحيـــض:
40- عن عائشة رضي الله عنها "أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سألت النبي صلى الله عليه وسلم، فَقَالت: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فقالَ: لاَ، إِنَّ ذَلِكَ دَمُ عِرْقٍ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ اْلأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلَّى".
وفي رواية: "وَلَيْسَتْ بِالْحَيْضَةِ، فَإِذَا أَقْبَلَتِ الْحَيْضَةُ فَاتْرُكِي الصَّلاَةَ فِيهَا، فَإِذَا ذَهَبَ قَدْرُهَا فَاغْسِلِي عَنْكِ الدَّمَ وَصَلِّي".

BABUN DA ZAI YI BAYANI A GAME DA HUKUNCIN JININ HAILA:
40- An karvo daga (Nana) Aishatu (R.A) tace haqiqa Faximatu xiyar Abi Hubaishin ta tambayi annabin Allah (S.A.W.) sai tace (da shi): (Ya ma'aikin Allah) ni mace ce da nake yawan zubar jinin haila bani da tsarki shin ko na bar yin sallah? Sai ma'aiki (S.A.W.) yace da ita a'a, (ai ba kya bari ba) domin ai shi wannan wani jinin da yake zubowane daga wata jijiya (dake jikin mahaifa), sai dai ke abin da ya wajaba kiyi shine ki bar yin sallah gwargwadon kwanakin da kikeyin hailarki a ciki, sannan kuma sai ki yi wanka ki ci gaba da yin sallarki.
Amma a cikin wata ruwayar kuma cewa yayi (ai shi wannan jini ba jinin haila bane). Ke dai idan hailarki ta zo sai ki bar yin sallah a cikinta idan kuma gwargwadon yadda kike yin ta ya wuce sai kiyi wanka ki ci gaba da yin sallah.

 

 
41-وعن عائشة رضي الله عنها "أَنَّ أُمَّ حَبِيبَةَ اسْتُحَيْضَتْ سَبْعَ سِنِينَ، فَسَأَلَتْ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم عَنْ ذَلِكَ؟ فَأَمَرَهَا أَنْ تَغْتَسِلَ، فَكَانَتْ تَغْتَسِلُ لِكُلِّ صَلاَةٍ".
41-An karvo daga Nana Aisha (R.A) tace Ummu Habibata ta kasance ta yi jinin istahala har na tsawon shekara bakwai (daganan) sai ta tambayi ma'aikin Allah (S.A.W.) akan haka? Sai shi kuma ya umarce ta da yin wanka sai ya zamo ta kasance tana yin wanka ga kowacce sallah (wato bata haxa sallah biyar da alwala xaya).

 
42-وعن عائشة رضي الله عنها قالت: "كُنْتُ أَغْتَسِلَ أَنَا ورسولُ الله صلى الله عليه وسلم مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ كَلاَنَا جُنُبٌ. وَكَانَ يَأْمُرُنِي فَأَتَّزِرُ، فَيُبَاشِرُنِي وَأَنَا حَائِضٌ.وَكَانَ يَخْرِجُ رَأْسَهُ إِلَيَّ وَهُوَ مُعْتَكِفٌ، فَأَغْسلُهُ وَأَنَا حَائِضٌ".
42-An karvo daga Nana Aishatu (R.A) tace ni na kasance ina yin wanka ni da ma'aikin Allah (S.A.W.) a cikin qwarya xaya, kowanne xayanmu yana da janaba, sannan ya kasance yana umartata sai in xaura zani shi kuma sai ya rungumeni alhali ina haila. Hakanan kuma ya kasance yakan turo min kansa a yayin da yake ittikafi (a masallaci) sai ni kuma in wanke masa alhali ina haila.
43-وعن عائشة رضي الله عنها قالت: "كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَتَّكِئُ فِي حِجْرِي وَأَنَا حَائِضٌ، فَيَقْرَأُ الْقُرْآنَ"
43-An karvo daga Nana Aishatu (R.A) tace manzon Allah (S.A.W.) ya kasance yana kashingixa akan cinyata alhali ina haila yakan kuma karanta alqur'ani yana kuma kashingixan akan cinyar tawa.
44- وعن مُعاذة قالت: "سألت عائشة رضي الله عنها فقلت: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَوْمَ وَلاَ تَقْضِي الصَّلاَةَ؟ فقالت: أحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ فَقلت: لَسْتُ بِحَرُورِيَّة، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ، فقالت كان يُصِيبُنَا ذَلِكِ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ وَلاَ تُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلاَةِ".
44-An karvo daga Ma'azata (R.A) tace (wata rana) na tambayi (Nana) Asihatu (R.A) sai nace da ita wai shin mai yasa ne mai jinin haila zata rama azumi ba zata rama sallah ba? Sai kuwa Nana Aisha tace (da ita) au ko kema kina daga cikin masu aqidar Haruriyyanci ne? (wato Khawarijawa) sai ita kuma tace a'a, a'a, ko kaxan ni ba mai bin aqidar Haruriyyanci ba ce, sai dai kawai ni ina tambayane kawai (Daga nan sai ita Nana Aishar) tace mun kasance irin wannan xin yana samun mu sai kawai a umarcemu da mu rama Azumi amma ba'a umatarmu da rama sallah.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka