An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna legit.ng Jul 29, 2019 5:49 AM Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya ga ta kansa yayin da rikici ya kaure a filin wasan kwallon kafa ta Ahmadu Bello dake garin Kaduna, ABS, inda har sai da Yansanda suka dinga harba barkonon tsohuwa a cikin jama’a. Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli bayan an kammala wasan karshe na gasar AITEO Cup tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes. Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasan ya kai ga bugun daga kai sai gola sakamakon kunnen doki da aka tashi, daga karshe Kano Pillars ta samu nasara da ci 4-3, sai dai magoya bayan Pillars sun shiga fili a guje don murna, inda jami’an tsaro suka taresu, daga nan fa sai rikici ya kaure, shine dalilin da yasa Yansanda suka shiga harba barkonon tsohuwa. Daga cikin wadanda rikicin ya rutsa dasu akwai gwamnan jahar Kano da ya je goy aba Pilla
An ƙirƙiri wannan shafine don ilimintarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa, wa'azantarwa akan Al'amuran "sadarwa"