Skip to main content

Addu'o'i Managarta Masu Albarka

Adu'o'i Masu Fa'ida Da Albarka, من الكتاب الحسن المسلم


  • Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Fita Daga Bandaki. غُفْرَانَكَ. Ghufranak. Ya Allah! Gafararka (na ke nema)

  • Zikiri yayin fara Alwala. بِسْمِ اللهِ. Bismi l-lahi Zikiri Bayan Gama Alwala أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ. Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne. kuma اَللَّهُـمَّ اجْعَلْنِـي مِنَ التَّـوّابِينَ وَاجْعَـلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّـرِينَ. Allahummaj-alnee minat-tawwabeena waj'alnee minal-mutatahhireen. Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka. 15. سُبْحَـانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْدِكَ أَشْهَـدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ . Subhanakal-lahumma wabihamdika ashhadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa-atoobu ilayka. Tsarki ya tabbata gare Ka ya Allah tare da yabo gare Ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafarka kuma ina tuba gareKa.

  • Zikiri Yayin Fita Daga Gida بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللهِ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ. Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah. Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah. اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ أَنْ أَضِـلَّ أَوْ أُضَـلَّ ، أَوْ أَزِلَّ أَوْ أُزَلَّ ، أَوْ أَظْلِـمَ أَوْ أَُظْلَـمَ ، أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُـجْهَلَ عَلَـيّ . Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta. Zikiri Yayin Shiga Gida. بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا . Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna. Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.

  • Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci اللّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُورًا، وَفِي لِسَـانِي نُورًا، فِي سَمْعِي نُورًا، فِي بَصَرِي نُورًا، مِنْ خَلْفِي نُورًا، وَمِنْ أَمَامِـي نُورًا، وَ مِنْ خَلْفِي نُوراً، فِي نَفْسِي نُوراً، وَأَعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِّمْ نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً ، وَاجْعَلْنِي نُوراً، اَللُّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً ، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وَفِي بَشَرِي نُوراً ". "اَللَّهُمَّ اجْعَلْ لِي نُوراً فِي قَبْرِي .. وَنُوراً فِي عِظَامِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً. Allahumma j'al fi kalbi nuran, wa fi lisani nuran, wa fi sam'i nuran, wa fi basari nuran, wa min fawki nuran, wa min tahti nuran, wa 'an yamini nuran, wa 'an shimali nuran, wa min amami nuran, wa min khalfi nuran waj'al fi nafsi nuran, wa a'zim li nuran, wa 'azzim li nuran. Wa j'al li nuran, wa j'alni nuran. Allahumma a'tini nuran, wa j'al fi 'asabi nuran, wa fi lahmi nuran, wa fi dami nuran, wa fi sha'ri nuran, wa fi bashari nuran. (Allahumma j'al lin nuran fi kabri, wa nuran fi izami) (wa zidni nuran, wa zidni nuran, wa zidni nuran) (wa hab li nuran 'ala nur). Ya Allah ka sanya haske a cikin zuciyata, da haske a kan harshena, da haske a gabana, da haske a damana, da haske a haguna, da haske a gabana, da haske a bayana; Ka sanya haske a cikin raina, Ka girmama haske gare ni, ka girmama min haske, ka sanya haske gare ni, Ka sanya ni (na zama) haske, Ka sanya haske a cikin jijiyoyina, da haske a cikin namana, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fatata, Ya Allah Ka sanya mini haske a cikin kabarina, da haske a cikin kasusuwana, ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka ba ni haske a kan haske. Addu'ar Fita Daga Masallaci. بِسمِ الله وَالصّلاةُ وَالسّلامُ عَلى رَسولِ الله، اللّهُـمَّ إِنّـي أَسْأَلُكَ مِـنْ فَضْـلِك، اللّهُـمَّ اعصِمْنـي مِنَ الشَّيْـطانِ الرَّجـيم. Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasoolil-lah, allahumma innee as-aluka min fadlik, allahumma iAAsimnee minash-shayta nir-rajeem. Da sunan Allah tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ina rokonka daga falalarka. Ya Allah! Ka kare ni daga shaidan tsinanne.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...