Skip to main content

Posts

Showing posts from July, 2019

Halifofin Shehu Ibrahim Inyass Na Nigeria

Halifofin Shehu Ibrahim Inyanss Halifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannunsa ✍️ Rayyahi Sani Khalifa Akwai wasu daga cikin halifofin Shehu a Najeriya wadanda Allah yayi musu baiwa da samun mukadamanci kai tsaye daga hannun Shehu RA, kamar yanda na samu a cikin littafin ( رجال وادوار حول صاحب الفيضة ) wanda Sheikh Muhammad dan Shehu Abdullahi Altijani ya rubuta. A cikin wannan littafin mawallafin ya tattara sunaye da takaitattun bayanai akan kowani Shehi, da kuma ainihin wasiqar/shahadar da Shehu ya rubutawa kowanni daya daga cikinsu na mukaddamanci. Wadannan shehunnai su ke da izini mudlaqi na bada darika da mukadamanci da bada izinin karanta asraran tijjaniyya ga wanda suka ga dama a kuma lokacin da suka ga dama daga wajen Shehu RTA. Wadannan dai sune tushen Faidha a Najeriya dan haka muridai da sauran al'umma ku sani cewa duk wani abu da ake danganta shi da faidha idan bai fito daga wadannan zawiyoyin ba ko rasan da su

Yadda Zaka Samu Space A wayarka, Bayan Tacika

YADDA ZAKA SAMU 'MORE SPACE' AWAYARKA TA ANDROID, BAYAN TA CUSHE Assalamu Alaikum yaa Ƴan uwana Maza da Mata ma'abota bibiyarmu awannan Shafi mai Albarka. A yau made, da ikon Allah mun zomuku da wata tsarabar wadda zata amfane ku wajen magance matsalar da take addabar ku Awayoyinku, na ƙaraci Space. Yayi dai dai ASHA KARATU LAFIYA..... Kamar yadda kuka sanine sau da yawa mutun zaga bashi da wani Abu (files, images, apps, videos, music, e.t.c) da yawa akan wayarka amma kanaso ka Sauko da wani abu ko Atura maka, kawai sai wayar tace maka (is not enough space delet some), to In sha Allahu nesa tazo kusa. Kawai matakin farko da zakabi har ƙarshe shine:- 1. Ka shiga menu na wayarka. 2. Sai file manager 3. Danna internal memory 4. Shiga Home 5. Zaɓi ko shiga memory na kan Wayar 6. Ka duba duk folders da kake da su 7. Wanda kaga akwai wani abu mai amfani, sai ka bar shi, ko kuma ka Select (zaɓi), sai ka dubu duk inda kaga ansa alamar Almakashi, saika taɓa shi, koda g

Ganduje Da Mataimakan Gwamnoni Uku Sun Tsalake Rijiya Da Baya

An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna legit.ng Jul 29, 2019 5:49 AM Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya ga ta kansa yayin da rikici ya kaure a filin wasan kwallon kafa ta Ahmadu Bello dake garin Kaduna, ABS, inda har sai da Yansanda suka dinga harba barkonon tsohuwa a cikin jama’a. Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli bayan an kammala wasan karshe na gasar AITEO Cup tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes. Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasan ya kai ga bugun daga kai sai gola sakamakon kunnen doki da aka tashi, daga karshe Kano Pillars ta samu nasara da ci 4-3, sai dai magoya bayan Pillars sun shiga fili a guje don murna, inda jami’an tsaro suka taresu, daga nan fa sai rikici ya kaure, shine dalilin da yasa Yansanda suka shiga harba barkonon tsohuwa. Daga cikin wadanda rikicin ya rutsa dasu akwai gwamnan jahar Kano da ya je goy aba Pilla

Falalar Goma Farko Na Zul-Hajji

*Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji* An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: Ranar Daya Ga Watan zilhijja ita ce Ranar Da Allah (swt) ya Gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk Wanda Ya Azimci Wannan Rana Allah(SWT) zai Gafarta Masa kowane irin zunubi tsakaninsa da shi. (2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan Rana yana da lada kwatankwacin wanda ya Raya shekara da ibada . (3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan Rana Allah (SWT) zai karbi Adduo’insa. (4) Ranar Hudu Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya Azimci wannan Rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu. (5) Ranar Biyar Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya Azimci Wannan Rana Allah (SWT) zai kare shi daga munafunci ko azab

Saƙon Wata ƙungiyar Yorubawa ga 'Makiyaya'

Labaran Siyasa Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya ▷ Nigeria news | Legit.ng Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya Naziru Dalha Taura Afenifer, babbar kungiyar 'yan kabilar Yoruba, ta umarci Fulani Makiyaya da ke yankin kudu maso yamma da su gaggauta barin yankinsu ko kuma su fuskanci fushinsu, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito ranar Alhamis. Yayin wani taro da manema labarai da shugabannin kungiyar suka yi a Legas, Afenifere ta roki majalisun kasa da kar su canja dokar da zata bawa gwamnatin tarayya ikon karbar filaye daga gwamnatin jihohi domin yin tsarin Ruga. Da yake karanta jawabi amadadin sauran shugabannin kungiyar, Dattijo Ayo Adebanjo, ya ce ba zasu yarda kashe-kashen da ake yi a yankin ya cigaba ba. Ragowar shugabannin kungiyar da suka halarci taron sun hada da Banji Akinto

Kamfanin Samsung Galaxy, Ya Ƙera Wayar Da Za A Iya Naɗeta

[x]Kamfanin Samsun Galaxy Ya Gabatar Da Wayar Da Yaƙera, wacce Zaka iya Naɗeta, bayan Kammala gyaran Allonta (screen), bayan tsayar da Aikin da yayi tun Awatan Disambar Bara. [x]Samsung's shine kamfanin waya na farko da ya fara ƙewa smartphone, wanda za a iya naɗeta kuma ka sarrafata yadda kake so. [x] Tun farkwon fara aiwatar da tsarin sai ya samu damuwa. [x]An sake gabatar da shirin a watan Afrilu bayan da masu sa ido na farko suka bayar da rahoton karyayyun fuska.(broken screen) [x]Samsung ya ce ya inganta na'urar kusan $ 2,000 ($ 1,603) wacce za a sayar a wasu zaɓaɓɓun kasuwanni. [x]Kamfanin ya yi tsere don ƙaddamar da layin wayar hannu kafin abokan hamayyarsa. [x]A sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce Samsung ya dauki lokaci ne don yin cikakken nazarin kan tsarin samar da abubuwan da suka dace da kuma gudanar da gwaje-gwaje masu tsauri. [x] Don Haɓaka kayansa, ya sanya tare da shimfida yanki mai kariya don tabbatar da shi ba tare da ancire shi ba, [x]kazalika y

Samsung Galaxy Folding Phone Ready

Samsung Galaxy Fold 'ready' for launch after screen fix 2 hours ago Share this with Facebook Share this with WhatsApp Share this with Messenger Share this with Twitter Share DJ Koh, President and CEO of IT & Mobile Communications Division of Samsung Electronics, announces the new Samsung Galaxy Fold smartphone during the Samsung Unpacked event on February 20, 2019 in San Francisco, California.Image copyrightGETTY IMAGES Samsung's first foldable smartphone will go on sale in September after problems with the device delayed its initial release. The April launch of the Galaxy Fold was postponed after early reviewers reported broken screens. Samsung said it had made "improvements" to the nearly $2,000 (£1,603) device which would be sold in "select markets". The firm has been racing to launch a folding smartphone before its rivals. "Samsung has taken the time to fully evaluate the product design, make necessary improvements and run rigorous tests

Jagoran Hajji Da Ummara kashi 1

HAUSA JAGORAN MAHAJJACI DA MAI UMARA Wallafar Ɗalal bn Ahmad al-‘Aqeel Gabatarwar Mai Girma Shaikh Salih bn Abdul’Aziz bn Muhammad Aal-al-Shaikh Shaikh Salih bn Abdul’Aziz bn Muhammad Aal-al-Shaikh []Yabo da godiya su tabbata ga Allah wanda ya farlanta hajin Ɗakin Allah mai alfarma ga wax anda suke da iko daga cikin bayinSa, kuma Ya sanya aikin Haji kuvutacce ya zama kankarace ga zunubai da laifuffuka. Salatin Allah da amincinSa su tabbata ga za- vavven Annabi, fiyayyen wanda yayi Ɗawafi da sa’ayi, kuma mafi girman wanda yayi talbiya kuma yayi addu’a. Wannan salati da aminci su tabbata har ga iyalan gidansa da sahabbansa da wanda ya bishi da kyautatawa kuma yayi koyi dashi. Bayan haka, ya xan uwana Alhaji mai daraja, ina maka maraba da lale zuwa wannan qasa mai aminci, kuma ina roqon Allah – Tsarki ya tabbata a gar- eShi - ya sauqaqe maka gudanar da ibadarka ta aikin haji da umara ta fuskar da Allah zai yarda da ita, kuma Allah ya sanya aikin ya zama da ikhlasi domin All

Shari'ar Atiku Da Buhari: Wani Mai Bada Shaida Ya Fashe Da Kuka

LABARAN SIYASA® Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu by Muhammad Auwal An sha mamaki a yayin zaman kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa na 2019 a lokain da wani shaidan jam’iyyar PDP, da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar ya fashe da kuka a gaban kotu yayin da yake amsa tambayoyi daga lauyan shugaban kasa Buhari. Shaidan mai suna Muhammed Arume Yahaya, wanda shine jami’in tattara sakamakon zabe na jam’iyyar PDP a mazabar Abocho cikin karamar hukumar Dekina ta jahar Kogi ya fashe da kuka ne a lokacin da yake bayanin yadda tashe tashen hankula da aka yi a yayin zaben suka hanashi gudanar da aikinsa. KU KARANTA: Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun ya tambayi Yahaya ko ya san abinda ya faru a akwatin zabe a lokacin da ya tsere don tsira daga harbe harben da yace wasu m

Maye Ake Nufi Da "Ethical Hacking"?

Meye “Ethical Hacking” Kuma? Daga Taskar Baban Sadik Kalmar “Hacking” dai kamar yadda mun sha bayanai a kai, shi ne amfani da kwarewa a fannin na’urori da hanyoyin sadarwa, don isa ga bayanai dake wata na’ura, wanda a al’adance ba kowa ke iya isa gare su ba. Ko amfani da kwarewa wajen iya sarrafawa da kuma mallake na’urori da hanyoyin sadarwa cikin sauki. Idan aka ce: “Hack” a turancin sadarwa na zamani, yana iya daukan ma’anar amfani da kokari na musamman wajen ganin “kwakwaf,” kan yadda wata na’ura ko wata hanya ta sadarwa ke aiki. Wannan halattacciyar ma’anar wannan kalma kenan. To amma da tafiya tayi nisa, sai ma’anarta a kwakwalen mutane ta canza, saboda samuwar masu amfani da wannan kwarewa wajen aiwatar da ta’addanci ga kwamfutoci ko na’urorinsu, ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani. Wannan yasa da zarar ka ji ance “Hacker” ko “Hacking,” nan take ba abin da zuciyarka za ta hararo maka sai aikin ta’addanci ta hanyar sadarwa, ko wani dan ta’adda a fagen sadarwa na zamani;

DABARUN ƳAN DAN-DATSA DA HANYOYIN DAƘILESU

DA BARUN ƳAN DANDATSA DA HANYOYIN Dakile Su (5) FASAHAKARIYAR BAYANAI By: Baban Sadik Last Updated Jul 18, 2019 Daga Taskar Baban Sadik kashi na biyar cikin jerin kasidun da muke kawowa kan hanyoyin da yan dandatsa ke bi wajen aiwatar da ta’addancinsu ga kwamfutocin jama’a. A sha karatu lafiya. Darasi Na (02): “Scanning Networks” Bayan darasi kan yadda ake tattaro bayanai kan kwamfuta ko kamfani ko wata na’urar da ake son isa gare ta. A darasi na biyu mai take: “Scanning Networks,” ana karantar da dalibai ne yadda zasu yi amfani da bayanan da suka samo daga wancan bincike, wajen isa ga wata kwamfuta ko na’ura ta musamman da suka samo adireshi ko sunanta. Kafin nan, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, duk wata kwamfuta da kake iya isa gareta a tsarin sadarwa na zamani, tana ajiye ne a wani zangon sadarwa na musamman, dake wani wuri na musamman, a wata kasa ko jiha ko gari na musamman, cikin ginin wani kamfani ko ofishi ko gida ko daki na musamman. Wannan zango shi ake kira: “L

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#

AKWAI VIRUS A WAYARKA

AKW A I VIRUS A WAYARKA KA SANI KUWA? Daga: duniyarwaya Kamfanin tsaro na NQ ya kama sabuwar kwayar cuta mai suna a.privacy.COMmal.c . Da zarar cutar ta kama na'urarka, cutar ta kan aika abubuwa ba tare da izini ba 1. Tura sakonni zuwa lambobin ka koda baka bukaci hakan ba. 2. Kuma ya aika bayanan sirri, irin su lissafin lambobi da kuma Kira rajistan ayyukan zuwa adireshin imel da aka aiko shi. 3. Yakan lura da ayyukanka sannan yana cinye files

Yadda Zaka Haɗa Istagram, facebook, twitter da Sauran Zaurukan Sada Zumunta

HADA INSTAGRAM DA TWITTER KO SAURAN ZAURUKAN SADA ZUMUNTA   March 26, 2018     0 Kamar yadda  Instagram  ya shahara haka kuma yake da tarin mabiya, sannan mafi yawa daga mabiyansa suna ta'ammali da zaurukan sada  zumunta kamar twitter da sauran su, balle kuma  facebook  wanda dama shi ne mai mallakin  instagram , yayinda kusan kaso 90% na masu  account a  Instagram  suna yin  facebook . To bisa ga yadda ake yin post, wani yafi Bukatar yayi post a Instagram sannan yana da account da wani zauren amma sai kaga acan ba'a tattaunawa dashi.  Wannan rubutu zai fahimtar damu yadda zaka hada Instagram dinka da wasu zaurukan sada zumunta, inda duk lokaxin da kayi post a daya daga cikin zaurukan, mabiyanka na kowanne zaure zasu ga abinda kayi post hoto, bidiyo, ko rubutu. Misali idan ka hada Instagram dinka da twitter to idan kayi rubutu a Instagram to abokanka na Twitter zasu gani, hakan idan kayi a twitter, na instagram dinka zasu gani. Idan kana bukatar hada

Waiwaye Game Da Batun Almajirci

WAIWAYE Game Da Batun Bara, Almajirai Da Makarantun Allo Dags Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheik Nasiru Kabara 1- Batun almajirai da makarantun tsangaya, ba ni da ja cewa akwai illoli da ke bukatar gyara a lamarin, amma ina ganin ya kamata mu bi a sannu, saboda wadannan dalilai:- a) Na lura kungiyoyi masu angizon kasashen turai sun himmatu matuka da farmaki kan lamarin karatun Qur'ani na tsangaya da almajirai, shekara da shekaru suna kamfen da furofaganda don kishiyantar lamarin. Na kasa gano maslaharsu cikin kokarinsu na gyara mana tsarimmu na karatun Qur'ani, saboda nai imani ba sa son Qur'anin ba sa son mu, kuma ba zasu kashe ficikarsu kan zallar maslaharmu ba! Ina so na gane meye maslaharsu cikin gyara tsarin karatun Qur'animmu, anya babu wata dasisa a boye? b) Mas'alar almajirai da tsangaya daya ce daga jerin mas'alolin da wadannan kungiyoyi da sauran masu tasirantuwa da Turawa ke fafutuka a kai, kamar daidai

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

Yadda Ake sarrafa hoto a kwamfuta

Assalamu alaikum, yaa ƴan uwana ma'abota, bibiyar mu a wannan shafi mai albarka®√ Da fatan dai kuna jin daɗin tate da amfanuwa da Darusan mu. ¤••••100% Yau da yardar Allah Darasin mu zaiyi bayani ne akan yadda ake sarrafa Hoto A Kwamfuta (photorshop) ⏳---__-----_-------_----__--_-----___-___--__-🔛 Marquee Tool (kayan aiki na marqee) Ana amfani da alamar kayan aikinne don yin zaɓi a kan hotonmu, wanda za a iya kwafe shi, yankewa, canza launinsa, motsawa ko wani abu kamar yadda muka soyi.  Akwai samfurori guda huɗu daban-daban na alama, Su ne, Alamar layin rubutu Ana amfani da kayan aiki na rectangular marquee don zaɓar siffar rectangular na hoton.  Alamar alamar martaba Alamar elliptical za ta iya ɗauka duk wani wuri mai launi daga siffar mu.  Lissafi na jeri guda ɗaya Alamar layi guda ɗaya za ta iya zaɓin guda ɗaya a kwance daga siffarmu.  Alamar maɓalli guda ɗaya Wannan alamar shafi guda ɗaya zai iya zaɓin guda ɗaya daga cikin hotunan mu.  STEPS:  Bude wa