Skip to main content

Hukunci Wanda Yayi Zina Da Wadda Ba Musulmaba

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA.

Hukuncinka daidai yake da na kowanne mazinaci.


Da farko dai kaci amanar kanka Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi.
Sannan kaci amanar hukumar Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al ummar wani yankin da ba naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin.


Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari ar musulunci?.

Kaima kasan bashi da hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku dakai dashi.
Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin muminan kirki awajen Allah.
Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen Allah, yana ha data waje guda ne tare da shirka da kisan kai.
Sune laifuka uku mafiya girma a Musulunci.
Allah yana magana acikin Alqur ani game da siffar bayinsa na kwarai, yace : SUNE WADANDA BASU KIRAN WANI ABIN BAUTA TARE DA ALLAH KUMA BASU KASHE WANI RAI WANDA ALLAH YA HARAMTA SAI DAI DA HAKKI, KUMA BASU YIN *ZINA.* WANDA YA AIKATA WANNAN ZAI HADU DA UQUBA (KO KUMA ZA A JEFASHI ACIKIN WATA RIJIYA ACIKIN JAHANNAMA, MAI SUNA ATHAM .
ZA A NINNINKA MASA AZABA ARANAR ALQIYAMAH, KUMA ZAI DAWWAMA ACIKINSA, ACIKIN HALIN WULAKANTUWA .
Malamai irin su Ikrimah sun ce acikin Jahannama akwai wasu ramuka guda biyu masu suna Gayyu da Atham acikinsu ake jefa mazinata da sauran masu biye wa sha awa anan duniya.
Ibnu Abid dunya ya ruwaito wani hadisi ta hanyar Haitham bn Malik Atta eey (Allah ya yarda dashi) yace Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : BAYAN SHIRKA BABU WANI ZUNUBI MAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DA MANIYYIN DA MUTUM YA SANYA ACIKIN MAHAIFAR DA BATA HALATTA GARESHI BA . Don Qarin bayani aduba tafseerin Ibnu Katheer, Suratul Furqan ayah ta 68-70.
Ga kuma hadisin da Bukhary da Muslim ta Tirmidhiy suka ruwaito ta hanyar Sahabbai daban daban, wanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace MAZINACI BA ZAIYI ZINA ALHALI YANA MUMINI BA (WATO YAYIN DA MAZINACI YAZO ZAI YI ZINA, ANA CIRE MASA IMANI NE DAGA ZUCIYARSA).
Idan laifin zina ya tabbata akan saurayi musulmi, ko kuma yayi furuci da kansa cewa yayi zina, to hukuncinsa shine bulala dari kamar yadda ayar cikin suratun Nur ta bayyana.
Don haka nake yi maka nasihar cewa kaji tsoron Allah ka tuba zuwa gareshi. Shi Allah mai karbar tuban bayinsa ne. Ka nisanci zina da duk abinda ya shafeta. Kaje kayi aure ka runtse idanuwanka daga kallon haram ko aikata haram. Domin akwai ranar da Allah zai tambayi kowacce ga bar jikinka akan dukkan aikin da ka aikata da ita.
Allah yace SAI DAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA AIKATA AYYUKA NA KWARAI .

WALLAHU A ALAM.

kayi sharing domin mafiyawan Matasanmu sun abka cikin wannan balai ko Allah zaisa kaima ta dalilin ka koda mutun dayane ya samu shiriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...