Skip to main content

Yadda zak Goge ko Dakatar Da Facebook Ɗinka

Yadda za a goge asusun Facebook na dindindin a cikin matakai 3 masu sauƙi

James Laird |

Dalian da suke Mutun tunanon share facebook account ɗinsa Sune kamar haka:-

Ko dai kana damuwa da wasu sirri kanka ta yanar gizo, ko kuma kawai kana gajiya da sabuntar shigar yau da kullun daga abokai na Mu'amula, ko abokai na makaranta, waɗanda ka fahimci cewa a zahiri basu da kyaky-kyawan hali, akwai wasu dalilan da yawa, da yasa zaka so ka share asusun Facebook din ka - kuma yin hakan ba shi da wahala In sha Allahu, ba kamar yadda mitane suke tunani ba.

A cikin wannan maƙalar, zamuyi bayanin yadda zaka share Facebook-mataki-mataki, gami da bayyana bambanci tsakanin 'Dakatar da asusun', da kuma goge shi gaba daya.

Idan kana tunanin share asusunka to ba kai bane farau.

Hakan na faruwane sakamakon ɓacin rai game da tasirin matsalolin kafofin watsa labarun da ke shafar lafiyar mutum da rayuwarmu, da yawa mutane sukan ci gaba da juya baya ga waɗannan rukunin yanar gizon da suka mamaye yanar gizo.(masu kawowa mutun damuwa).

To Koma dai maye dalilinka, na sharewa ko tsaida asus ka, to a zahiri abu ne mai sauki.

Akwai hanyoyi daban-daban guda biyu don samun asusun Facebook naka a layi. Na farko shine kashewa, wanda ke nufin: Zaku iya sake amfani da asusunku a duk lokacin da kuke so

Mutane ba za su iya ganin Facebook timeline dinku ba, ko kuma nemanku(search)

Sai dsi akwai Wasu bayanan da zasu ka sance a bayyane (kamar sakonnin da kuka aiko) Facebook yana adana bayanan asusunku (kamar abokai. da abubuwan sha'awa) idan kua sake kunnawa (dawo da asusun naka

Amma share asusunka wani lamari ne mai matukar muhimmanci, Idan ka buƙaci hakan

Idan ka Share asusunka: Facebook yakan ɗan jinkirta sharewa na ƴan kwanaki bayan an nemi bukatar ko zaka canza shawara, Idan lokacin ɓacinran ya wuce, amma idan aka riga aka goge kwakwata kwakwata tofa Ba za ka iya sake samun damar dawowa da asusunka na Facebook ba.

Amma sukan baiwa mutun kamar kwanaki 90 kafin agama share bayananku da ke cikin ma'ajiya

Don kashe asusun Facebook naka, bi waɗannan matakan guda huɗu:-

  • 1. Danna menu na ƙasa a saman hannun dama na kowane shafin Facebook a cikin manemar yanar gizanka (browser)
  • 2. Zaɓi 'Saiti'
  • 3. Zaɓi 'Janar' a cikin ɓangaren hagu
  • 4. Danna 'Gudanar da asusunka'
  • 5. Latsa 'Kashe asusunka', sannan ka bi matakan tabbatar da shawarar ka Don sake maido asusunka bayan ka dakatar da shi, kawai shiga cikin Facebook imel ɗin ka, sai kasa kalmar sirri.

Sai dai Bayanan ba zaka iya sake dawo da shi gaba dayaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...