TUNATARWA WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA FALALAR WANKAN GAWA Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’ A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace: ”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin). SHARUDDAN WANKAN GAWA: Daga cikin sharaddan wankan gawa sune: {1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali: Iyaye. kanne ko yayyek “ya”yansa da sauransu). {2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta). {3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi. YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali: Sau Uku (3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9). Hakan ya tabbata daga Manzon Al
An ƙirƙiri wannan shafine don ilimintarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa, wa'azantarwa akan Al'amuran "sadarwa"