Skip to main content

Posts

Showing posts from August 20, 2019

Tsarin Fasahar Fai fai DVD (1)

TSARIN FASAHAR FAI FAIFAN DVD (1) A kashi na uku mai karatu ya ci karo ne da bayanai dalla-dalla kan kimiyya da fasahar da suke qunshe cikin faifan CD, da falle-falle da aka sarqafe wuri xaya don inganta tsarin zubawa da sarrafa bayanai cikin sauki. Ahalin yanzu za mu ci gaba, inda za mu tavo fasaha ta gaba, wato: Faifan DVD. Matashiya Makonni uku da suka gabata muka fara gabatar da bayanai tiryan-tiryan kan tsarin ma’adanar bayanai, daga na dauri zuwa waxanda muke amfani dasu a wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa. A babin matashiya, mun gabatar da bayani kan hanyoyin da xan adam ya biyo a baya wajen taskance bayanai a tsarin da ya samu kansa a ciki; da irin ci gaban da ya samu daga baya – daga haddace abubuwa zuwa rubutu da karatu. Mai karatu ya qara ji har wa yau, sadda xan adam ya fara dogaro da ci gaban qere-qere wajen adana bayanansa. Kashi na biyu ya leqa xakin tarihi ne, inda na naqalto mana tarihi da asalin faifan tangaraho, da faifan CD, wanda a harshen tura