Skip to main content

Posts

Showing posts from July 19, 2019

Shari'ar Atiku Da Buhari: Wani Mai Bada Shaida Ya Fashe Da Kuka

LABARAN SIYASA® Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu by Muhammad Auwal An sha mamaki a yayin zaman kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa na 2019 a lokain da wani shaidan jam’iyyar PDP, da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar ya fashe da kuka a gaban kotu yayin da yake amsa tambayoyi daga lauyan shugaban kasa Buhari. Shaidan mai suna Muhammed Arume Yahaya, wanda shine jami’in tattara sakamakon zabe na jam’iyyar PDP a mazabar Abocho cikin karamar hukumar Dekina ta jahar Kogi ya fashe da kuka ne a lokacin da yake bayanin yadda tashe tashen hankula da aka yi a yayin zaben suka hanashi gudanar da aikinsa. KU KARANTA: Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun ya tambayi Yahaya ko ya san abinda ya faru a akwatin zabe a lokacin da ya tsere don tsira daga harbe harben da yace wasu m