Skip to main content

Ganduje Da Mataimakan Gwamnoni Uku Sun Tsalake Rijiya Da Baya

An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna legit.ng Jul 29, 2019 5:49 AM

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya ga ta kansa yayin da rikici ya kaure a filin wasan kwallon kafa ta Ahmadu Bello dake garin Kaduna, ABS, inda har sai da Yansanda suka dinga harba barkonon tsohuwa a cikin jama’a.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli bayan an kammala wasan karshe na gasar AITEO Cup tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasan ya kai ga bugun daga kai sai gola sakamakon kunnen doki da aka tashi, daga karshe Kano Pillars ta samu nasara da ci 4-3, sai dai magoya bayan Pillars sun shiga fili a guje don murna, inda jami’an tsaro suka taresu, daga nan fa sai rikici ya kaure, shine dalilin da yasa Yansanda suka shiga harba barkonon tsohuwa.

Daga cikin wadanda rikicin ya rutsa dasu akwai gwamnan jahar Kano da ya je goy aba Pillars baya, akwai kuma mataimakan gwamnonin Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, na jahar Neja, Muhammad Ketso, da na Nassarawa, Eammnuel Akabe, kuma sauran manyan baki da dama.

Rikicin ya yi kamari ne bayan yan kato da gora sun shiga dukan magoya bayan Kano Pillars da gorori, inda suma magoya bayan Pillars suka sake shiri suka tunkari yan sa kai, aka yi ta fafatawa, da kyar Yansanda suka kori kowa daga cikin filin da barkonon tsohuwa.

Sai can bayan kura ta lafa shine shuwagabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya yi rabon lambobin yabo ga yan wasan da kungiyoyinsu, amma a lokacin kusan babu kowa a filin, ba kamar yadda ya yi cikar farin dango ba a yayin da ake doka wasan.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...