Skip to main content

Falalar Goma Farko Na Zul-Hajji

*Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji*

An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce:

Ranar Daya Ga Watan zilhijja ita ce Ranar Da Allah (swt) ya Gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk Wanda Ya Azimci Wannan Rana Allah(SWT) zai Gafarta Masa kowane irin zunubi tsakaninsa da shi.

(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan Rana yana da lada kwatankwacin wanda ya Raya shekara da ibada .

(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan Rana Allah (SWT) zai karbi Adduo’insa.

(4) Ranar Hudu Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya Azimci wannan Rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu.

(5) Ranar Biyar Ga Zulhijja ita ce Ranar Da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya Azimci Wannan Rana Allah (SWT) zai kare shi daga munafunci ko azabar kabari.

(6) Ranar shida ga Zilhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) ya yi Budin Alkhairi Ga Annabi (SAW). Duk Wanda ya Azimci Wannan Rana Allah zai dube shi da Rahama, kuma ba zai azabtar da shi ba.

(7) Ranar bakwai Ga Zulhijja ita ce Ranar Da Allah (SWT) zai sa a Rufe kofofin wuta, ba za a bude su ba har sai Wadannan kwanaki Goma sun wuce. Duk wanda ya Azimci Wannan Rana Allah zai Rufe masa kofofi talatin na tsanani a Rayuwarsa a buda masa kofofi talatin na sauki.

(8) Ranar Takwas Ga Zilhijja ita ce Ranar da ake cewa, Ranar tarayya. Duk wanda ya Azimci wannan Ranar, babu wanda ya san A Dadin Ladarsa sai Allah.

(9) Ranar tara ga Watan Zulhijja ita ce Ranar Hawan Arfa. Allah yana Gafartawa Duk Alhazan da ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya Wurin Aikin Hajji, idan ya Azimci Wannan Ranar, Allah yana Gafarta masa zunibinsa na shekarar Da ta Gabata, Da kuma shekarar Da ke tafe.

(10). Ranar Goma Ga Zulhijja ita ce Ranar layya. Duk wanda Allah ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka Dabbarsa, Digon jini Na farko Da zai fara diga a kasa zai zama Gafara Gare shi Da iyalinsa.

An so Wanda zai yi layya Da wanda ba zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan An Dawo Daga Sallah idi, ya ci abinci ko wani abu daga cikin layyarsa. Allah zai ba shi lada wacce ta fi Dutsen Uhud Girma Da Nauyi. Kuma ana so ya Raba Namansa kashi uku. Kashi Na farko Sadaka, kashi Na biyu kyauta, kashi Na uku kuma Domin iyali.

Allah Ya Bamu Ikon Azumtar Dukkan Wadannan Ranakun, kuma ya sadamu Da Falalar Da ya Tanadar Ga Masu Ibada A Wadannan Ranaku. Ameen Ya Allah.
✍Daga Dahiru Salihu*

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka