Skip to main content

Posts

Showing posts from July 31, 2019

Halifofin Shehu Ibrahim Inyass Na Nigeria

Halifofin Shehu Ibrahim Inyanss Halifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannunsa ✍️ Rayyahi Sani Khalifa Akwai wasu daga cikin halifofin Shehu a Najeriya wadanda Allah yayi musu baiwa da samun mukadamanci kai tsaye daga hannun Shehu RA, kamar yanda na samu a cikin littafin ( رجال وادوار حول صاحب الفيضة ) wanda Sheikh Muhammad dan Shehu Abdullahi Altijani ya rubuta. A cikin wannan littafin mawallafin ya tattara sunaye da takaitattun bayanai akan kowani Shehi, da kuma ainihin wasiqar/shahadar da Shehu ya rubutawa kowanni daya daga cikinsu na mukaddamanci. Wadannan shehunnai su ke da izini mudlaqi na bada darika da mukadamanci da bada izinin karanta asraran tijjaniyya ga wanda suka ga dama a kuma lokacin da suka ga dama daga wajen Shehu RTA. Wadannan dai sune tushen Faidha a Najeriya dan haka muridai da sauran al'umma ku sani cewa duk wani abu da ake danganta shi da faidha idan bai fito daga wadannan zawiyoyin ba ko rasan da su