Skip to main content

Posts

Showing posts from July 26, 2019

Saƙon Wata ƙungiyar Yorubawa ga 'Makiyaya'

Labaran Siyasa Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya ▷ Nigeria news | Legit.ng Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya Naziru Dalha Taura Afenifer, babbar kungiyar 'yan kabilar Yoruba, ta umarci Fulani Makiyaya da ke yankin kudu maso yamma da su gaggauta barin yankinsu ko kuma su fuskanci fushinsu, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito ranar Alhamis. Yayin wani taro da manema labarai da shugabannin kungiyar suka yi a Legas, Afenifere ta roki majalisun kasa da kar su canja dokar da zata bawa gwamnatin tarayya ikon karbar filaye daga gwamnatin jihohi domin yin tsarin Ruga. Da yake karanta jawabi amadadin sauran shugabannin kungiyar, Dattijo Ayo Adebanjo, ya ce ba zasu yarda kashe-kashen da ake yi a yankin ya cigaba ba. Ragowar shugabannin kungiyar da suka halarci taron sun hada da Banji Akinto