Skip to main content

Posts

Showing posts from August 18, 2019

Hukunci Wanda Yayi Zina Da Wadda Ba Musulmaba

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA. Hukuncinka daidai yake da na kowanne mazinaci. Da farko dai kaci amanar kanka Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi. Sannan kaci amanar hukumar Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al ummar wani yankin da ba naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin. Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari ar musulunci?. Kaima kasan bashi da hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku dakai dashi. Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin muminan kirki awajen Allah. Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen Allah, yana ha data waje guda ne tare da shirka da kisan kai. Sune laifuka uku mafiya girma a Musulunci. Allah yana magana acikin Alqur ani game da siffar bayinsa na kwarai, yace : SUNE WADANDA BASU KIRAN WANI ABIN BAUTA TAR