Skip to main content

Maganin Yawan Fitar Ruwa Mai Kai-kayj Afarjji



Ga Mata masu lalurar fitar ruwa masu Kaikayi daga Farjin su. 


A gwada daya daga cikin wadannan:-

1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.


2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.


.
3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection.
.



4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.



5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.



6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni’ima.



7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.



8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su tay Yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni’ima da magance duk
matasalolin sanyi.



9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.



10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni’ima.



11) A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
12-Asamu garin saiwar Zogale se a debi cokali daya adafashi da ‘yar jan kanwa se adinga sha. Yana maganin fitar Ruwa ta gaba sosai ***
Yan uwa Mata sai a jaraba. 



Comments

Popular posts from this blog

Waiwaye Game Da Batun Almajirci

WAIWAYE Game Da Batun Bara, Almajirai Da Makarantun Allo Dags Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheik Nasiru Kabara 1- Batun almajirai da makarantun tsangaya, ba ni da ja cewa akwai illoli da ke bukatar gyara a lamarin, amma ina ganin ya kamata mu bi a sannu, saboda wadannan dalilai:- a) Na lura kungiyoyi masu angizon kasashen turai sun himmatu matuka da farmaki kan lamarin karatun Qur'ani na tsangaya da almajirai, shekara da shekaru suna kamfen da furofaganda don kishiyantar lamarin. Na kasa gano maslaharsu cikin kokarinsu na gyara mana tsarimmu na karatun Qur'ani, saboda nai imani ba sa son Qur'anin ba sa son mu, kuma ba zasu kashe ficikarsu kan zallar maslaharmu ba! Ina so na gane meye maslaharsu cikin gyara tsarin karatun Qur'animmu, anya babu wata dasisa a boye? b) Mas'alar almajirai da tsangaya daya ce daga jerin mas'alolin da wadannan kungiyoyi da sauran masu tasirantuwa da Turawa ke fafutuka a kai, kamar daidai...

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s...