Skip to main content

YADDA AKE WANKAN GAWA

TUNATARWA

WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA


FALALAR WANKAN GAWA

Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’


A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace:

”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin).


SHARUDDAN WANKAN GAWA:

Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:

{1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali: Iyaye. kanne ko yayyek “ya”yansa da sauransu).

{2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta).

{3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi.


YADDA AKE YIN WANKAN GAWA

Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali:


    Sau Uku (3) ko
    Biyar(5) ko
    Bakwai(7) ko
    Tara(9).

Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (s.a.w) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A).

Wadanda za su yiwa mamaci wanka su zasuyi la’akari suga wanka nawa yadace suyi masa.

Da farko dai kafin a fara wankan da akwai abubuwa guda Uku (3) da za’a fara yi wa mamacin.

Sune kamar haka:

{1}. Za’a cire masa suturar da take jikinsa, amma za’a sami dan kyalle a rufe masa al’aurarsa.

{2}. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na bangaren mafuta biyu.
(Bawali da Gayadi).
{3}. Idan macece , za’a tsefe kitson da yake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba guda Uku).
Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba daya.

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3) Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama saisu fara wankan. Da farko dai zasu tanadi ruwa kashi Uku (3), kowanne ruwa za'ayi wanka daya dashi. (RUWAN FARKO) Wannan wankan za'ayi wa mamacine wanka irin Wankan Janaba. Da farko za’a fara yiwa mamaci alwalane, kamar irin alwalar Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da shakar hanci za’a shafa masa ruwane kawai a bakin da hancin. Bayan anyi masa alwala, sai kuma azuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan. kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu. (RUWA NA BIYU) Bayan anyi masa wanka na sama wato na Janaba, sai kuma asami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin dashi.
Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, saidai za’a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun).
Bayan angama cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan. (RUWA NA UKU) Bayan anyi masa wanka na sama, wato na Soso da Sabulu, to sai kuma a sami ruwa na karshe wato na Uku a zuba Turare mai kamshi (Sosai) a ciki, sannan sai a wanke mamaci da shi.
Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to amma idan ba’a same shiba to za’a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai. Bayan angama wankan Turaren, sai a tsane jikin mamacin asa masa Likkafani.

YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7), KO TARA (9). Idan masu yi wa mamaci wanka sun zabi su yi masa wanka biyar (5), ko bakwai(7), ko tara(9). To wanka na biyu(2) wato na soso da sabulu shi za su yi ta maimaitawa. Amma dolene na Janaba shine a Farko, sannan na Turare shine a karshe.

MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU BIYAR (5).


{1}. Na farko shine na Janaba

{2}. Na biyu shine na soso da sabulu

{3}. Na uku shine na soso da sabulu

{4}. Na Hudu shine na Soso da Sabulu

{5}. Na Biyar shine na Turare.

YA UBANGIJI KASA MU CIKA DA IMANI AMIN.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ake Raba Hard-Disk Gida Biyu ko Fiye Da Haka

«HOW TO CREATE A PARTITION» Daga:Arewa Computer YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c. Anayin ‪#‎partition‬ ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu. Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko ‪#‎START_MENU‬ *Sannan kaje kan ‪#‎MY_COMPUTER‬ kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT *Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na ‪#‎DISK_MANAGEMENT‬ zai fito maka da DRIVE dinka wato ‪#‎Harddisk‬ naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a. *Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi ‪#‎right_click‬ a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:- ‪#‎Open‬ ‪#‎Explore‬ ‪#‎Mark_partition‬ as Active ‪#‎Change_Drive_Letter‬ and paths ‪#‎Format‬ ‪#...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...