Skip to main content

Posts

Showing posts from November 15, 2019

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci