Skip to main content

Posts

Showing posts from August 8, 2019

Kayan Aikin Gina Manhajar Kwamfuta Kashi na1

Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta (1) A Kashi na bakwai cikin binciken da muke yi kan tsarin gina manhajar kwamfuta. A sha karatu lafiya. Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta Kafin aiwatar da kowane irin aiki, Magina manhajar kwamfuta na bukatar kayan aiki. Wadannan kayayyakin aiki suna da yawa, dangane da girma ko mahimmancin manhajar da ake son ginawa. A tare da haka, akwai wadanda suke wajibi ne, akwai kuma wadanda samuwarsu abin so ne, ba wajibi ba. Ga wasu daga cikin kayayyakin aikinsu nan: Ilimi da Kwarewa: Wannan shi ne abu na farko. Magina manhajar kwamfuta kwararru ne, wadanda suka san kan kwamfuta da rayuwarta, da lafiyarta, da makisanta. Sanayya a wannan mahanga abin so ne wajen gina manhajar kwamfuta. Wannan ilimi kuwa ya hada da kwarewa a fagen dabarun gina manhajar da ake son amfani da shi. Ba dole bane sai ka san dukkan dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages), a a. Misali, kana iya gina manhajar kwamfuta da na wayar salula ta amfani da