Skip to main content

ƘUNGIYAR MANOMA TAYI MAGANA

MANOMA: DAGA YANZU BUHUN SHINKAFA BA ZAIWUCE 15,000 BA.

By: Muhammadu Auwal Umar A korarin karfafa wa gwamnatin tarayya na hana fasakaurin shinkafa a kasar nan, kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya ta ce, daga yanzu buhun shinkafa ba zai wuce naira 15,000 ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamin a garin Abuja, shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIPAN), Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya.
Ya kara da cewa, shinkafar gida da ake yi a Nijeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000. Kungiyar ta bayyana cewa, ta rubuta wa gwamnatin tarayya wasika wajen karya farashin shinkafa, domin ta karfafa wa gwamnati wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan. Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Nijeriya tana asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin.
Alhaji Mohammed Abubakar Maifata tare da matemakinsa Mista Paul Eluhaiwe sun bayyana cewa, sun kammala tuntubar mutanensu da ke bakin iyakar kasar nan. Shugaban kungiyar RIPAN ya ci gaba da cewa, akwai tan 500,000 na shinkafa da ake kan hanyar shigo da su kasar nan daga Thailand kafin bikin kirsimeti. A cewar shugaban kungiyar, ba shakka wannan zai sa masu fasakaurin shinkafa su yi asarar dala miliyan 4000. A bangaransa, rufe iyakar da ke tsakanin Nijeriya da kasar Benin zai taimaka wajen dakile fasakaurin shinkafa tare habbaka shinkafar gida.
Ya kara da cewa, kungiyar tana goyan bayan gwamnatin tarayya wajen kulle iyakar kasar nan. Kungiyar ta babbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za ta saka wa ‘ya’yan kungiyar haraji domin ta cike gurbin farashin shinkafa a kasuwa, sakamakon rufe iyakar kasar nan. Ta kara da cewa, kasar nan tana bukatar tan miliyan hudu na shinkafa a duk sheka, amma mambobin kungiyar za su shigo da shinkafa wanda ya kai tan miliyan biyar.
Mohammed Abubarkar ya ce, “tun daga watan Junairu har zuwa yau, ba a shigo da shinkafar da ta kai miliyan daya ba daga kasar Jumhuriyan Benin da Thailand da kuma India zuwa Nijeriya ta haramtacciyar hanya.
Ya kara da cewa, mafi yawancin shinkafar da ake shigowa da ita daga kasar Benin, ‘yan kasar Benin ba sa amfani da wannan shinkafa shi ya sa ake kawota Nijeriya. Lokacin da aka rufe iyakar kasar nan, ‘ya’yan kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, “daga yau saun dauki damarar noman shinkafa yadda ya kamata.”
Mohammed Abubarkar ya ce, kungiyarsa sun kwashe sama da shekara biyu suna neman a rufe iyakar kasar nan, saboda su sauko da farashin shinkafa. A cikin bayanin da ya gabatar ranar Laraba a garin Abuja, mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina, ya bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa, zai dauki mataki a kan masu safarar shinkafa lokacin da ya hadu da shugaban kasar Benin a kasar Japan. Shugaban kasar ya kara da cewa, ayyukan masu fasakaurin shinkafa yana kawo barazana ga tsarin da gwamnatinsa take yi wajen bunkasa harkokin noma.
A cewar shugaba Buhari, “a yanzu mutane suna komawa karkara domin su ci gaba da noma gonakinsu, kasar tana samun kudadan shiga, maimakon amfani da shinkafar kasar waje. Ba za mu taba barin yarda a ci gaban da fasakaurin kayayyakin ba,” in ji shi. Shugaban Nijeriya ya ce, mukasudin rufe iyakar kasar nan shi ne, ‘yan Nijeriya su bunkasa kayayyakin gida.
Tun da farko dai, shugaban kasar Benin Talon ya bayyana cewa, ya yi kira ga shugaban Nijeriya sakamakon alfanun da mutanen kasar suka samu game da rufe iyakar kasar.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka