Skip to main content

Tsarin Fasahar Fai fai DVD (1)

TSARIN FASAHAR FAI FAIFAN DVD (1)

A kashi na uku mai karatu ya ci karo ne da bayanai dalla-dalla kan kimiyya da fasahar da suke qunshe cikin faifan CD, da falle-falle da aka sarqafe wuri xaya don inganta tsarin zubawa da sarrafa bayanai cikin sauki.

Ahalin yanzu za mu ci gaba, inda za mu tavo fasaha ta gaba, wato: Faifan DVD.


Matashiya

Makonni uku da suka gabata muka fara gabatar da bayanai tiryan-tiryan kan tsarin ma’adanar bayanai, daga na dauri zuwa waxanda muke amfani dasu a wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa. A babin matashiya, mun gabatar da bayani kan hanyoyin da xan adam ya biyo a baya wajen taskance bayanai a tsarin da ya samu kansa a ciki; da irin ci gaban da ya samu daga baya – daga haddace abubuwa zuwa rubutu da karatu. Mai karatu ya qara ji har wa yau, sadda xan adam ya fara dogaro da ci gaban qere-qere wajen adana bayanansa. Kashi na biyu ya leqa xakin tarihi ne, inda na naqalto mana tarihi da asalin faifan tangaraho, da faifan CD, wanda a harshen turance ake kira: “Compact Disc.”


A kashi na uku mai karatu ya ci karo ne da bayanai dalla-dalla kan kimiyya da fasahar da suke qunshe cikin faifan CD, da falle-falle da aka sarqafe wuri xaya don inganta tsarin zubawa da sarrafa bayanai cikin sauki.


A halin yanzu za mu ci gaba, inda za mu tavo fasaha ta gaba, wato: Faifan DVD.


Faifan DVD

Haruffan “DVD” na ishara ne ga kalmar: “Digital Versatile Disc”. Fasaha ce ta taskancewa da kuma sarrafa bayanai nau’uka daban-daban, ta hanyar hasken lantarki nau’in leza (Laser Light), wanda ke xauke cikin faifan gasasshen roba. Wannan suna na “DVD” shi ne sunan da kwamitin samar da wannan fasaha ya bashi, a farkon lamari, ba tare da tantance hakikanin abin da haruffan ke nufi ba. Wannan ya jawo savanin ma’anoni da lafuzza tsakanin kamfanonin da ke da alhakin qera waxannan faya-fayai da ake son fitarwa a lokacin. Kamfanin Toshiba yace ma’anar lafuzzar DVD a wajensa ita ce: “Digital Video Disc”. Abin da wannan ke nufi shi ne – idan aka yi la’akari da wannan ma’ana – kamfanin na nuna cewa an samar da wannan fasaha ne kawai don fa’idar taskancewa da kuma sarrafa bidiyo zalla.


Wannan yasa sauran kamfanonin qera kwamfutoci a lokacin suka ce basu yarda da wannan suna mai xauke da wannan ma’ana ba. Domin su ma suna da ruwa da tsaki wajen qerawa da kuma yaxa wannan fasaha, tunda kwamfutocin da suke qerawa suna xauke da na’urar dake sarrafa faifan DVD, kamar yadda suke xauke da na’urar sarrafa CD a baya. Don haka, a cewarsu, dole ne ayi amfani da kalmar “Digital Versatile Disc”, wato: “Fasahar dake iya taskancewa da sarrafa nau’ukan bayanai daban-daban na zamani, mai juriya da qwazo wajen adana su da kuma miqo su, a duk sadda aka buqace su.” Daga qarshe dai, dole kamfanin Toshiba ya haqura, ya koma amfani da haruffan DVD mai ma’anar: “Digital Versatile Disc”.


Abin da wannan ke nufi shi ne, faifan DVD ma’adana ce wacce ake iya zuba bayanai nau’in rubutu (Text), da sauti (Audio), da daskararren hoto (Still Image/Picture), da hoto mai motsi, wato bidiyo (Video), da taswira (Map), da bayanan bayanai (Metadata), da kuma manhoji ko masarrafan kwamfuta (Applications/Programs). Bayan an taskance su a ciki, sannan ana iya amfani da na’urar DVD (DVD Player ko DVD-ROM da DVD-RW dake kwamfuta), wajen sarrafa waxannan bayanai, cikin sauqi. Bayan iya xaukan kowane nau’in bayanai, faifan DVD na da mizani mai girma, fiye da mizanin faifan CD, wacce bayaninta ya gabata a baya.


To, laifin me kuma faifan CD tayi, da har aka mata kishiya a duniyar fasahar sadarwa na wancan zamani?


Asali da Samuwar Faifan DVD a Duniya

Faifan DVD ta samo asali ne a shekarar 1995, bayan dusashewar hasken faifan CD, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Duk da cewa faifan CD da ma DVD da aka samar duk suna amfani ne da hasken lantarki nau’in leza wajen taskance bayanai da kuma sarrafa su, idan aka jefa su cikin na’urar dake iya fahimtar yarensu, sai dai ba su bane farkon fasahar da aka fara amfani dasu wajen aiwatar da wannan tsari na ta’ammali da bayanai.


Fasahar taskance bayanan bidiyo, musamman, ta amfani da hasken lantarki (wanda ba nau’in leza ba) ya samo asali ne a shekarar 1958, inda wasu bayin Allah masana harkar qere-qere da sadarwa irin na wancan zamanin suka samar da wata fasaha mai iya taskance saqonnin bidiyo ta hanyar hasken lantarki. Waxannan bayin Allah dai su ne: Mista David Paul Gregg da abokinsa Mista James Russel. Hukumar lura da fasahar qere-qere ta qasar Amurka ta basu rajistar wannan fasaha ne (Patent) a shekarar 1961. Wanda wannan ne ya tabbatar musu da cikakken haqqin mallaka kan wannan fasaha.
Ana shiga shekarar 1978 kuma sai fasaha makamanciyar wancan, mai suna: “LaserDisc” ta bayyana a birnin Georgia ta jihar Atlanta dake qasar Amurkan dai, har wa yau. Wannan fasaha dai faifai ce, irin wacce muka yi bayaninta kuma muke kan yi a yanzu, amma wannan tana da girma sosai. A taqaice dai faifai ne. Sai dai fasahar bata shahara ba a dukkan qasashen duniya, kamar yadda fasahar Faifan CD ta shahara. Wannan ya faru ne sanadiyyar xan karen tsada da take dashi a wancan lokaci; ba kowa ke iya mallakar fasahar ba. Har wannan sabuwar fasaha ta gama zamaninta, qasashen Jafan, da Koriya ta Kudu, da qasashen Turai, da Hong Kong, da Singafo, da Malesiya da kuma lardin Taiwan ne kaxai suka yi ta’ammali da ita.
Zuwa shekarar 1987 sai kamfanin Philips da Sony suka samar da fasahar faifan CD, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Wannan ita ce fasahar farko da aka qirqira a duniya, wacce ke iya taskance bayanai musamman na bidiyo, ta amfani da hasken lantarki nau’in leza. Da tafiya tayi nisa, fasahar faifan CD ta fara ja baya saboda ci gaban zamani, wannan dalili na farko kenan. Dalili na biyu shi ne, fasahar faifan CD ba ta xaukan bayanai mai yawa. Duk bayanan basu wuce mizani biliyan 750 ba. Wannan, ta la’akari da yanayin zamanin da ake ciki a lokaci, basu taka kara bai balle su karya. Dalili na uku shi ne, fasahar faifan CD ba ta tsawon rayuwa; ba ta da qarko. Da zarar fuskar faifan ta samu matsala, na’urar ba ta iya karanto bayanan dake cikin faifan.
Waxannan dalilai suka sa a shekarar 1993 kamfanin Sony da Philips suka yi yunqurin samar da wata sabuwar fasaha wacce a tunaninsu ta zarce fasahar faifan CD qarko da qarin mizani sama da 750MB. Sun samar da wata fasaha mai suna: “Multimedia Compact Disc” (MMCD), wato fasahar faifan CD mai iya xaukan kowane irin nau’in bayani da taskance shi. Wannan a vangaren kamfanin Sony da Philips Kenan, waxanda daman tun a farko su ne masu xabbaqa fasahar ma’adanar bayanai da sadarwa a fannin bidiyo da sauti.
A dai wannan shekara har wa yau kuma sai ga wata fasahar sabuwa ful, mai suna: “Super Density” Disc, wato “SD” kenan a taqaice. Waxanda suka samar da wannan fasaha dai kamfanoni ne guda 7, kuma su ne kamar haka: Toshiba, da Time Warner, da Matsushita Electric, da Hitachi, da Mitsubishi Electric, da Pioneer, da Thomson da kuma JVC. Waxannan dai kamfanoni ne na qere-qere a fannin lantarki da sadarwa. Kuma ta la’akari da wancan sabuwar fasaha ta MMCD, akwai savabin tsari da yanayin taskance bayanai. Wannan na nufin idan an fara qera faifan wannan fasaha za a samu matsala kenan.
Ana cikin haka sai haxakar kamfanonin kwamfuta guda biyar, a cikin watan Agusta na shekarar 1995, suka yi zuga don nuna rashin amincewarsu da wannan tsari bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya. Waxannan kamfanoni dai su ne: kamfanin IBM, da kamfanin Apple, da kamfanin Compaq, da kamfanin Hewlette-Packard, sai kuma kamfanin kwamfuta na Microsoft. Waxannan kamfanoni dai sun qi amincewa ne da savanin dake tsakanin waxancan fasahohi guda biyu, kuma suka ce dole ne a hade tsarin wadannan fasahohi guda biyu don samun tsari bai-xaya. Wannan gungu na kamfanonin kwamfuta dai sun naxa shugaban kamfanin IBM ne don jagorantar wannan kwamiti don tabbatar da samuwar biyan buqatarsu. Kuma cikin dacewar Allah, nan take aka samu amincewar kowane vangare; aka tabbatar da kundin fasahar DVD mai xauke da tsari xaya, da taskancewa da kuma sarrafa bayanai ta hanyar dukkan na’urorin da za a qera don aiwatar da hakan.

Daga: Taskar Baban Sadik

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka