Skip to main content

Posts

Showing posts from July 16, 2019

Waiwaye Game Da Batun Almajirci

WAIWAYE Game Da Batun Bara, Almajirai Da Makarantun Allo Dags Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheik Nasiru Kabara 1- Batun almajirai da makarantun tsangaya, ba ni da ja cewa akwai illoli da ke bukatar gyara a lamarin, amma ina ganin ya kamata mu bi a sannu, saboda wadannan dalilai:- a) Na lura kungiyoyi masu angizon kasashen turai sun himmatu matuka da farmaki kan lamarin karatun Qur'ani na tsangaya da almajirai, shekara da shekaru suna kamfen da furofaganda don kishiyantar lamarin. Na kasa gano maslaharsu cikin kokarinsu na gyara mana tsarimmu na karatun Qur'ani, saboda nai imani ba sa son Qur'anin ba sa son mu, kuma ba zasu kashe ficikarsu kan zallar maslaharmu ba! Ina so na gane meye maslaharsu cikin gyara tsarin karatun Qur'animmu, anya babu wata dasisa a boye? b) Mas'alar almajirai da tsangaya daya ce daga jerin mas'alolin da wadannan kungiyoyi da sauran masu tasirantuwa da Turawa ke fafutuka a kai, kamar daidai