Skip to main content

Yadda Zaka Samu Space A wayarka, Bayan Tacika

YADDA ZAKA SAMU 'MORE SPACE' AWAYARKA TA ANDROID, BAYAN TA CUSHE Assalamu Alaikum yaa Ƴan uwana Maza da Mata ma'abota bibiyarmu awannan Shafi mai Albarka.

A yau made, da ikon Allah mun zomuku da wata tsarabar wadda zata amfane ku wajen magance matsalar da take addabar ku Awayoyinku, na ƙaraci Space.

Yayi dai dai
ASHA KARATU LAFIYA.....
Kamar yadda kuka sanine sau da yawa mutun zaga bashi da wani Abu (files, images, apps, videos, music, e.t.c) da yawa akan wayarka amma kanaso ka Sauko da wani abu ko Atura maka, kawai sai wayar tace maka (is not enough space delet some), to In sha Allahu nesa tazo kusa. Kawai matakin farko da zakabi har ƙarshe shine:-
1. Ka shiga menu na wayarka.
2. Sai file manager
3. Danna internal memory
4. Shiga Home
5. Zaɓi ko shiga memory na kan Wayar
6. Ka duba duk folders da kake da su
7. Wanda kaga akwai wani abu mai amfani, sai ka bar shi, ko kuma ka Select (zaɓi), sai ka dubu duk inda kaga ansa alamar Almakashi, saika taɓa shi, koda gudawane kayi mark, danan sai ka shiga Sd Card ɗinka, idan kaso kai create new folder, in kuma kaso ka barshi a root na memory ɗin, sai taɓa Alamar ɗan wani box mai ɗugo-ɗugo,. 8. Idan kuma folders ɗin empty ne (ba komai), bayan ka Select (zaɓi) sai ka taɓa Alamar Almashinnan, 9. Shikenan zaka samu Space mai yawa akan wayarka.
10. Ka riƙa yin haka duk lokacin da kaso.
FAƊAKARWA:-

Su folders ɗin idan baka ga komi mai kyauba, to karji komai kawai ka share shi babu abinda zai faru

[x]Dafatan Allah ya sa mu dace

[x]Indai anji daɗi to yi Comment da "Maa sha Allah"

[x]Daga: Muhammad Auwal Umar

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka