WAIWAYE
Game Da Batun Bara, Almajirai Da
Makarantun Allo
Dags Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheik Nasiru
Kabara
1- Batun almajirai da makarantun tsangaya,
ba ni da ja cewa akwai illoli da ke bukatar
gyara a lamarin, amma ina ganin ya kamata
mu bi a sannu, saboda wadannan dalilai:-
a) Na lura kungiyoyi masu angizon kasashen
turai sun himmatu matuka da farmaki kan
lamarin karatun Qur'ani na tsangaya da
almajirai, shekara da shekaru suna kamfen
da furofaganda don kishiyantar lamarin.
Na kasa gano maslaharsu cikin kokarinsu na
gyara mana tsarimmu na karatun Qur'ani,
saboda nai imani ba sa son Qur'anin ba sa
son mu, kuma ba zasu kashe ficikarsu kan
zallar maslaharmu ba! Ina so na gane meye
maslaharsu cikin gyara tsarin karatun
Qur'animmu, anya babu wata dasisa a boye?
b) Mas'alar almajirai da tsangaya daya ce
daga jerin mas'alolin da wadannan
kungiyoyi da sauran masu tasirantuwa da
Turawa ke fafutuka a kai, kamar daidaiton
jinsi ko 'yancin mata da hakkokin yara da
auren wuri da auren dole da takaita
haihuwa.. da sauransu, wadanda mai
hankali kuma mai basira cikin addini in yai
tunani sai ya ga a hakika tsarin
zamantakewar Musulmi suke so su wargaza.
c) Mafi yawan illolin da ake fada na karatun
tsangaya in ban ce duka ba, akwai su ko
mafi muni daga gare su a makarantun
zamanin, kar dai wasu makarantun kwana
da jami'o'i da manyan kolejjoji su ji labari,
irin fasadin da ake da 'ya'yan jama'a
mazansu da matansu da yaduwar
kungiyoyin asiri.. da sauransu abu ne ba
boyaiye ba! Amma me ya sa ba a tono ire-
iren wadannan illoli da su ka mamaye
makarantun zamani a yake su, saidai a tasa
makarantun tsangaya a gaba su kadai?
d) Ana danganta wa almajirai miyagun
halaye iri-iri kamar shaye-shaye da sace-sace
da barazanar tsaro daga bala'in daba zuwa
na ta'addanci, ban ce ba sa yi ba, amma yaya
halin daliban makarantun zamani
musamman wadanda suka kare karatu
babu aikin yi daga 'yan sakandare zuwa
'yan jami'a, shin ba sa fadawa cikin
wadannan miyagun aiyukan?
2- Batu mafi hadari shi ne danganta
almajirai da tsangayu ga TA'ADDANCI,
wannan shaci-fadi ne da tsabar jahilci ko
zalumci.
Ta'addanci ba makarantun tsangaya ke
koyar da shi ba, ko an tsinci almajirai cikin
'yan ta'adda tsintar kansu suka yi ciki kamar
da sauran rukunai na mutane ke tsintar
kansu, don ba a tsangaya suka koya ba!
Ba alarammomi ke koyar da TA'ADDANCI ba,
ba kuma a makarantun tsangaya ake koyar
da shi ba, malaman WAHHABIYYAH ke koyar
da shi a makarantunsu duk fadin duniya.
Ina tambaya: a wace tsangayar Bin Ladan da
Al Zawahiri da Al Zarqawi da Al Bagdadi da
Al Aulaqi da Al Jaulani.. da sauransu duka
wadannan manyan 'yan ta'adda a wace
tsangaya su ka yi karatu? Wane alaramman
ne ya koyar da su? akwai almajiri guda a
cikinsu?
Dukkansu 'yan makaranta guda ne sunanta
WAHHABIYYAH, kuma dukkansu suna da
alaka da wata kasa guda wadda sunanta ke
farawa da harafin (S)!
Ta yaya basira zata bace a danganta
wannan kazamin aiki da ya game duniya
wato TA'ADDANCI wanda manyan
kungiyoyin leken asiri na wasu sanannun
kasashe ke ciyar da biliyoyin daloli don mara
ma sa baya da karfafa shi, ta yaya za a
danganta shi ga tsangayu da wadannan
miskinai masu karatu a tsangaya wato
almajirai, a halin ga miyagun 'yan ta'addan
na hakika saboda gatansu da tsabar
munafunci ko jahilci ko ambaton su ba a yi
wato WAHHABIYAWA!
3- Ita kanta Haj. Naja ta fadi cewa
makarantun islamiyyah da na boko sun
mamaye makarantun allo, kusan ma daga
zamaninsu an daina makarantun allon sai na
islamiyyah, duk da ina jin tuntuben harshe
ta yi, amma na yarda makarantun allo sun ja
baya sosai, na zamani kuma kullum habaka
suke yi, to ke nan ba zai hankaltu ba su
zama su ne babbar barazana ko cikas ga
al'uma, saboda sun yi rauni matuka, don
haka me ya sa suke tsone idon 'yan boko da
iyayensu Turawa suke ta babatu kansu?
A ganina maimakon zuguguta matsalar
makarantun allo da almajirai da bara, a
daidai lokacin da wadannan makarantu dab
su ke da gushewa, kamata ya yi duk wani
mai kishin al'uma ya mayar da hankalinsa
kan matsaloli na hakika da ke gabammu ba
matsaloli na jabu ba! A misali matsalolin
makarantun zamanin kansu, don a
fahimtata duk wata matsala da ake hange a
makarantun allo akwai irinta ko sama da ita
a makarantun zamani.
Kullum hankoro ake a gina sababbin
makarantu, kuma babatu ake cewa ba a sa
yara a makaranta.. Ina zaton a sakandarorin
jihar Kano kawai a shekara ana yaye dalibai
sama da dubu dari..
Ina makomar wadannan dubun dubatar
dalibai da ake yayewa?
Yaya ingancin karatu da tarbiyyar da ake ba
su?
Wane tsari aka yi mu su wanda al'uma zata
amfana da su, ko su amfana wa kansu?
Shin an tanadar mu su isassun gurabe a
jami'o'i da kolejoji don cigaba da
karatunsu?
Ko gomnati na sane da yawan daliban da
kolejoji da jami'o'i ke yayewa duk shekara,
shin ta tanadar mu su isassun guraben aiki
ko sana'a?
In ba a tanada ba, meye amfanin abunda
aka kashe mu su da wahalar da su ka sha ta
yin karatun shekara da shekaru?
Wai ma daga sanda aka soma karatun boko
kasar nan zuwa yau me ya tsinana mana in
banda magana ko rubutu da harshen
Bature?
Meye amfanin makarantun zamanin da aka
narka kazaman kudaden al'uma kansu, aka
shagaltar da 'ya'yansu ciki, amma sun gaza
haifar mana da al'umar da ke iya noma
abincin da za ta ci, ko suturar da za ta saka,
ko baburan hawanta ko motoci ko jiragen
sama ko na ruwa ko na kasa ko lantarki, ko..
ko.. ko.. kai ko burushi ko cokali, kai ko
allura..?
Kai, ban taba ganin kasa ko al'uma da take
tafe a makance kuma cikin duhu ba irin
tamu!!!
A karshe, duk mai son ya yaki TA'ADDANCI da
gaske to ya ci damarar yakar WAHHABIYYAH,
don a duk kasashen Musulunci babu DAN
TA'ADDA guda wanda ba BAWAHHABE ba!
Kuma duk mai kishin matasammu mai
fafutukar tsamo su daga aiyukan assha da
gurbacewar tarbiyya ya kwan da sanin cewa
baragurbi ba cikin almajiran tsangaya
kurum su ke ba, akwai su dankam cikin
daliban sakandare da kolejoji da jami'o'i,
don haka kar a takaita fafutukar gyara kan
makarantun tsangaya, a hada da
makarantun zamani zai ma fi kyau a fara da
su!
Kazamin abunda ya faru kimanin shekaru
biyu a wata mashahuriyar makarantar
sakandaren kwana a nan Kano ya ishe mu
misali.. Kuma ina gudun da za a yi bincike, a
makarantun zamani daga sakandare zuwa
jami'a, da an samu irin wannan barna ko
mafi muni daga gareta a makarantu da
dama.
Allah ya wadatar da mu.
Ya yi wannan bayani ne a watan Disamba,
2017.
@Nasiriyyah Social Media 25/06/2019.
Comments
Post a Comment