«HOW TO CREATE A PARTITION»
Daga:Arewa Computer
YADDA AKE RABA HARDDISK GIDA BIYU KO FIYE DA HAKA misali: C:, D:, E:, G: e.t.c.
Anayin #partition ne domin amfanin ajiya ko kuma kara dasa (INSTALLING) wani sabon Operating System da sauransu.
Da farko dai ka Danna maballin window (windows key) ko #START_MENU
*Sannan kaje kan #MY_COMPUTER kayi RIGHTS CLICK zaka ga MANAGE sai kayi selecting, zai bude maka wani window mai suna COMPUTER MANAGEMENT
*Cikin wannan window daga can kasa sai kayi selecting na #DISK_MANAGEMENT zai fito maka da DRIVE dinka wato #Harddisk naka dauke da GIRMANSA (size) da SUNA da abubuwanda ya kunsa (PRoperties) da kuma Format na wannan HARDDISK. Zaka ga yawan partition da ke kan HARDDISK naka idan ka taba rabawa ko ko a'a.
*Sannan ka zabi wanda kake son rabawa ko kuma kake son rage yawansa sai kayi #right_click a kansa zaka ga OPTIONS kamar haka:-
#Open
#Explore
#Mark_partition as Active
#Change_Drive_Letter and paths
#Format
#Extend_Volume
#SHRINK_VOLUME
#Add_Mirror
#Delete_Volume
#Properties
#Help
*Sai ka zabi #SHRINK_VOLUME sannan kajira dakika yan kadan wani window dan karami mai dauke da suna SHRINK zai bayyana Sannan za kaga Options masu yawa a gabansu akwai akwatina, kawai jeka izuwa ENTER THE AMOUNT OF SPACE TO SHRINK IN MB
Sai ka rubuta iya yawan abinda kake so sabon Drive dinka ya kasance, cikin wannan akwatin da ke gabansa. Misali: 56320 idan 50GB (GigaByte) kake so ko 158720 idan 150GB.
NOTE: kasani cewa 1024MB (MegaByte) shine 1GB dan haka sai ka lissafa kowani 1024MB nawane zai baka iya yawan GigaByte da kake bukata.
*Bayan ka rubuta iya abinda kake so za kaga #SHRINK sai ka danna ta. Zakaga sabuwar fili (Space) mai dauke da launin baki an rubuta #UNALLOCATED_SPACE.
*sai kaje kansa (UNALLOCATED SPACE) ka danna RIGHT_CLICK akansa sai kayi selecting #FORMAT zai nuna maka options da yawa: wajen #Drive_letter sai ka zabi wanda kake so,sannan
wajen #Drive_Format ka zabi #NTFS
Wajen #Drive_label sai ka baiwa Drive naka Sunan da kake so Sannan ka danna #FORMAT ko #Ok.
Shi kenan za kaga sabuwar fili (space/Drive) mai launin shudi (Blue) wanda kayi creating.
*Rufe windown Disk Management sannan ka danna maballin Window hade da E (Windows key+E)=Windows Explorer ko kuma kaje #My_Computer zakaga sabuwar Drive da kayi creating.
#NOTE (Lura da kyau) yayinda kake rage/raba Harddisk naka tabbatar ka rage iya abinda ya saura maka na drive din da kake son ragewa/rabawa kada kace zaka rage abinda yawuce ragowar drive (Free Space)

Comments
Post a Comment