Skip to main content

Jagoran Hajji Da Ummara kashi 1

HAUSA JAGORAN MAHAJJACI DA MAI UMARA Wallafar Ɗalal bn Ahmad al-‘Aqeel

Gabatarwar

Mai Girma Shaikh Salih bn Abdul’Aziz bn Muhammad Aal-al-Shaikh

Shaikh Salih bn Abdul’Aziz bn Muhammad Aal-al-Shaikh

[]Yabo da godiya su tabbata ga Allah wanda ya farlanta hajin Ɗakin Allah mai alfarma ga wax anda suke da iko daga cikin bayinSa, kuma Ya sanya aikin Haji kuvutacce ya zama kankarace ga zunubai da laifuffuka.

Salatin Allah da amincinSa su tabbata ga za- vavven Annabi, fiyayyen wanda yayi Ɗawafi da sa’ayi, kuma mafi girman wanda yayi talbiya kuma yayi addu’a. Wannan salati da aminci su tabbata har ga iyalan gidansa da sahabbansa da wanda ya bishi da kyautatawa kuma yayi koyi dashi.

Bayan haka, ya xan uwana Alhaji mai daraja, ina maka maraba da lale zuwa wannan qasa mai aminci, kuma ina roqon Allah – Tsarki ya tabbata a gar- eShi - ya sauqaqe maka gudanar da ibadarka ta aikin haji da umara ta fuskar da Allah zai yarda da ita, kuma Allah ya sanya aikin ya zama da ikhlasi domin Allah sannan ya zama bisa koyarwar AnnabinSa – sallallahu alaihi wa sallam.

Kuma ina roqon Allah ya karvi aikin sannan ya sanyashi cikin ma’aunin aikinka.

Ya ɗan uwana mahajjaci, idan kowace tawagar matafiya suna da shugaba, kuma kowane ayari yana da jagora mai nuna masa hanya, to lallai shugaban ayarin mahajjata shine Muhammadu – sallallahu alaihi wa sallam.

Kuma jagorar wannan ayari ita ce hanyarsa da sunnarsa. Domin kuwa shine mai cewa: “Ku riqi ibadar hajinku daga gareni”.

Domin haka ne ya zama dole ga duk mai nufin Ɗakin Allah domin Haji ko Umara ya koyi tsarin Annabi da kuma tafarkinsa – sallallahu alaihi wa sal- lam - ta hanyar amintattun littattafan koyarda ibadar Haji, da kuma tambayar malamai bisa duk abinda ya shige masa duhu.

To ya kai alhaji, ga wannan littafi gabanka wanda kalmominsa a bayyane suke, ya fito cikin sabon sunfuri, zai sauqaqa maka fahimtar hukunce huku- ncen haji da Umara da salon bayani quru-quru, tare da hotuna masu fito da komai filla-filla. Ina fata zaka xaukeshi a matsayin jagoranka a hajinka da umararka.

Lallai Ma’aikatar Al-amurran Musulunci ta Saudi Arabia tana murna da wannan matsayi da Allah ya bata na yi maka hidima ta baya- nin duk abinda zaka bukaceshi idan wani abu ya shige maka duhu, domin kuwa, ta tattali wasu cibiyoyi da rumfuna na musamman da 5 Mai Girma

*

Salih bn Abdul’Aziz Aal al-Shaikh zaka samu malaman da zasu nuna maka hanya, domin aiki da faxin Allah Ta’ala “Ku tambayi ma’abuta Ambato (ilimi) in ba ku sani ba”.

* A qarshen wannan shimfixa tawa, ba zan qarqareta ba sai na yi godiya mai tarin yawa ga xan uwana Shaikh Xalal bn Ahmad al-Aqeel wanda ya wal- lafa wannan littafin jagora. Kuma ina roqon Allah ya sanya wannan littafi da kuma dukkan wani kokari da gudumowa da wannan bawan Allah ya ke yi a wannan fage, ya sanyata cikin ma’aunan kyawawan ayyukansa, kuma ya kambama masa sakamakonsa da shi da abo- * kan aikinsa na kwamitin rabawa alhazai da masu umara littattafai da rubuce- rubucen addini da ke Jiddah, bisa wannan aiki mai albarka. Idan da wata wasiyya da zanyi maka ya baqon Xakin Allah, to zan maka wa- siyya tare ni kaina cewa ka ribaci wannan lokaci mai daraja wajen duk wani aiki da zai jawo yardar Allah wanda kazo a matsayin baqonSa, kuma ka sauka cikin iyakokin XakinSa, tare da barin duk abinda zai jawo fushinSa kuma ya ke qi. * Allah – Ta’ala – yana cewa:
{… kuma wanda yayi nufin ilhadi (karkata daga gaskiya) a cikinsa da zalunci zaMu xanxana masa wata azaba mai raxaxi.} [Suratul Haji: 25].
Ina roqon Allah ya sanya hajinka kuvutacce, aikinka abin godiya, zunubinka abin gafartawa. Salatin Allah da amincinSa da albarkarSa su tabbata ga bawanSa kuma man- zonSa, shugabanmu, abin koyinmu kuma abin qaunarmu Muhammadu, tare da iyanlan gidansa da Sahabbansa da masu biye musu. Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s

Bayanin Alwala Da Sallah

.                *FARILLAN ALWALA*  Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa  • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa  • Fyacewa  • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu  • Jeranta tsakanin farillah               *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah  • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni  • Qaranta ruwa a nisa gabobi  • Gabatar da dama kafin hau.                *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka