Skip to main content

Shari'ar Atiku Da Buhari: Wani Mai Bada Shaida Ya Fashe Da Kuka

LABARAN SIYASA® Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu by Muhammad Auwal An sha mamaki a yayin zaman kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa na 2019 a lokain da wani shaidan jam’iyyar PDP, da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar ya fashe da kuka a gaban kotu yayin da yake amsa tambayoyi daga lauyan shugaban kasa Buhari. Shaidan mai suna Muhammed Arume Yahaya, wanda shine jami’in tattara sakamakon zabe na jam’iyyar PDP a mazabar Abocho cikin karamar hukumar Dekina ta jahar Kogi ya fashe da kuka ne a lokacin da yake bayanin yadda tashe tashen hankula da aka yi a yayin zaben suka hanashi gudanar da aikinsa. KU KARANTA: Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun ya tambayi Yahaya ko ya san abinda ya faru a akwatin zabe a lokacin da ya tsere don tsira daga harbe harben da yace wasu matasa sun yi? Daga nan ne yasa kuka, inda yace an kashe masa abokai a dalilin harbin. Da fari dai Yahaya wanda yace mahaifiyarsa ce ta sanya masa suna ‘Honourable’ saboda ya zama babban dan siyasa yace ba’a yi zabe a rumfunan zabe guda 19 cikin 29 dake mazabarsa ba, don haka APC sun hada sakamakon zabe na bogi ne kawai. []Toh amma da lauyan Buhari, Olanipekun, lauyan INEC, Tanimu Inuwa da Lauyan APC, Lateef Fagbemi suka tambayeshi ta yaya ya san haka bayan yace ya boye a lokacin da aka fara harbe harbe? Sai ya basu amsa da cewa iyaka rumfuna 10 kawai ya iya zagayawa kafin a fara harbe harben, don haka bai san abinda ya faru a sauran ba bayan ya tsere. [x]Haka dai Yahaya ya cigaba da kuka yana zubar da hawaye ana bashi hakuri, da kyar Alkalin kotun, mai sharia Mohammed Garba ya shawo kansa inda ya rarrasheshi yana cewa “Ka daina kuka, mahaifiyarka da ta rada maka suna Honourable so take ka zama mai karfi, don haka ka daina kuka ka amsa tambayoyin.”

Daga nan Yahaya ya cigaba da zayyana ma kotu cewa mazabar Abocho waje ne da PDP keda karfi, da an cigaba da zaben cikin kwanciyar hankali da ta lashe zaben, amma da aka tambayeshi wa ya ci zabe a mazabar a shekarar 2015 sai ya kada baki yace APC.

Bugu da kari, Yahaya yace baya jin Hausa sai yaren Igala, amma lauyoyin APC sun tambayeshi ya aka yi aka sa hannunsa a kan sakamakon zaben da yace da Hausa aka fassara masa, anan ma sai ya kidime yace bai san yadda aka yi haka ba.

[] Ku biyo mu a Liget Hausa Facebook ko a Legit Hausa Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...