Skip to main content

Saƙon Wata ƙungiyar Yorubawa ga 'Makiyaya'

Labaran Siyasa
Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya ▷ Nigeria news | Legit.ng Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya
Naziru Dalha Taura

Afenifer, babbar kungiyar 'yan kabilar Yoruba, ta umarci Fulani Makiyaya da ke yankin kudu maso yamma da su gaggauta barin yankinsu ko kuma su fuskanci fushinsu, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito ranar Alhamis. Yayin wani taro da manema labarai da shugabannin kungiyar suka yi a Legas, Afenifere ta roki majalisun kasa da kar su canja dokar da zata bawa gwamnatin tarayya ikon karbar filaye daga gwamnatin jihohi domin yin tsarin Ruga. Da yake karanta jawabi amadadin sauran shugabannin kungiyar, Dattijo Ayo Adebanjo, ya ce ba zasu yarda kashe-kashen da ake yi a yankin ya cigaba ba.

Ragowar shugabannin kungiyar da suka halarci taron sun hada da Banji Akintoye, Femi Okunrounmu, Yinka Odumakin, Supo Shonibare da Sola Lawal. Adebanjo ya ce kungiyar Afenifere na bukatar Fulani makiyaya su gaggauta barin yankin kudu maso yamma ko kuma idan sun ki, jama'ar yamkin su yi 'fito na fito' da su.

Wani bangaren na jawabin kungiyar ya ce, "ba zamu yarda mutanen da suka ki yarda zababbun gwamnonin mu su kafa 'yan sandan jihohi ba yanzu kuma suke son karbar kasar mu domin yi wa makiyayan da suka hana mu zama lafiya wurin zama ba. "Mu na bukatar su gaggauta barin kasar 'yan kabilar Yoruba. Kuma idan suka ki yin hakan nan da dan wani lokaci, ba zamu hana mutanen mu yin 'fito na fito' da su ba."

Kungiyar ta kara da cewa ba zata yarda ta zuba ido ba a yayin da ake cigaba da zubar da jinin 'ya'yanta ba don kawai ana ikirarin zama a kasa daya mai bin tsarin tarayya ba. Kazalika, sun yi kira da a gaggauta koma wa tsarin mulki da ya bawa kowanne yanki damar cin gashin kansa.

nameMuhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Source: Legit.ng

Tags: YorubaHausa NewsRikicin MakiyayaAbun MamakiAbun Bakin Ciki

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...