Skip to main content

Yadda Zaka Haɗa Istagram, facebook, twitter da Sauran Zaurukan Sada Zumunta



HADA INSTAGRAM DA TWITTER KO SAURAN ZAURUKAN SADA ZUMUNTA



Kamar yadda Instagram ya shahara haka kuma yake da tarin mabiya, sannan mafi yawa daga mabiyansa suna ta'ammali da zaurukan sada  zumunta kamar twitter da sauran su, balle kuma facebook wanda dama shi ne mai mallakin instagram, yayinda kusan kaso 90% na masu  account a Instagram suna yin facebook.

To bisa ga yadda ake yin post, wani yafi Bukatar yayi post a Instagram sannan yana da account da wani zauren amma sai kaga acan ba'a tattaunawa dashi.  Wannan rubutu zai fahimtar damu yadda zaka hada Instagram dinka da wasu zaurukan sada zumunta, inda duk lokaxin da kayi post a daya daga cikin zaurukan, mabiyanka na kowanne zaure zasu ga abinda kayi post hoto, bidiyo, ko rubutu.

Misali idan ka hada Instagram dinka da twitter to idan kayi rubutu a Instagram to abokanka na Twitter zasu gani, hakan idan kayi a twitter, na instagram dinka zasu gani.
Idan kana bukatar hada instagram dinka da twitter ko wani zauren sada zumunta, saika tabbatar kana da account da su, sannan saika bi wadannan matakan:-

1. Ka bude Instagram dinka, a profile dinka saika taba
2. Idan iPhone ce da kai saika tabaIdan kuma Android ce taba 
3. Saika taba Linked Accounts, sannan ka taba zauren sada zumunta da kake bukatar ka hadesu "social network to log in and link the accounts"

Kana hadesu shi kenan, aduk lokacin da ka dauki hoto, bidiyo ko rubutu daga instagram zai bayyana a wadancan shafukan. Koda kuwa zauren sada zumuntar babushi a kasarka, misali akwai dandalin muhawara na wasu kasashe kadai,kamar irinsu China zaka samu suna da zaurukan sada zumunta na yankunansu.

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...