Skip to main content

Maye Ake Nufi Da "Ethical Hacking"?

Meye “Ethical Hacking” Kuma?

Daga Taskar Baban Sadik

Kalmar “Hacking” dai kamar yadda mun sha bayanai a kai, shi ne amfani da kwarewa a fannin na’urori da hanyoyin sadarwa, don isa ga bayanai dake wata na’ura, wanda a al’adance ba kowa ke iya isa gare su ba. Ko amfani da kwarewa wajen iya sarrafawa da kuma mallake na’urori da hanyoyin sadarwa cikin sauki. Idan aka ce:

“Hack” a turancin sadarwa na zamani, yana iya daukan ma’anar amfani da kokari na musamman wajen ganin “kwakwaf,” kan yadda wata na’ura ko wata hanya ta sadarwa ke aiki.

Wannan halattacciyar ma’anar wannan kalma kenan.

To amma da tafiya tayi nisa, sai ma’anarta a kwakwalen mutane ta canza, saboda samuwar masu amfani da wannan kwarewa wajen aiwatar da ta’addanci ga kwamfutoci ko na’urorinsu, ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani. Wannan yasa da zarar ka ji ance “Hacker” ko “Hacking,” nan take ba abin da zuciyarka za ta hararo maka sai aikin ta’addanci ta hanyar sadarwa, ko wani dan ta’adda a fagen sadarwa na zamani; wanda ke barkowa cikin kwamfutoci da na’urorin jama’a don sacewa ko gaurayawa ko jirkita bayanansu. Sanadiyyar yaduwar wadannan mutane masu mugun nufi, da yadda hakan ya canza wa jama’a ma’anarta a kwakwalensu, yasa aka samar da hanyoyin karantar da yadda za a dakile ayyukansu na ta’addanci, a halacce. Daga cikin fannonin dake karantar da hanyoyin dakile ayyukan ‘yan dandatsa akwai fanni mai take: “Ethical Hacking,” wanda cibiyar EC-Council ke koyarwa. Wanda ya samu horaswa kuma yaci jarabawa a wannan fanni, shi ake kira: “Certified Ethical Hacker” (CEH). A takaice dai, abin da “Ethical Hacking” ke nufi dai, shi ne: “Tsarin dandatsanci mai lasisi.” Shi kuma “Certified Ethical Hacker” ka kira shi: “Dan dandatsa mai lasisi.” An kira su da wannan suna ne saboda duk wanda ya mallaki shedar kammala wannan karatu zai iya zama ma’aikaci a fannin kariyar bayanai (Information Security). Sun sha bamban da wadanda ke amfani da kwarewar wajen aiwatar da ta’addanci. Duk aikin iri daya ne. Bambancin dake tsakaninsu shi ne, wadancan ‘yan ta’adda ne masu yi da mugun nufi. Su kuma wadannan masu shedar karatu da shedar kwarewa, suna dakile ayyukan wadancan ne, da izinin masu ma’aikata ko kamfanin da kwamfutocin suke. Daukansu ake yi na musamman, don baiwa kwamfutocin dake wata ma’aikata ko masana’anta ko kampani, kariya ta hanyar kwarewarsu. Bayani kan haka na tafe in Allah ya so.

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...