Skip to main content

DABARUN ƳAN DAN-DATSA DA HANYOYIN DAƘILESU

DA BARUN ƳAN DANDATSA DA HANYOYIN Dakile Su (5) FASAHAKARIYAR BAYANAI By: Baban Sadik Last Updated Jul 18, 2019 Daga Taskar Baban Sadik

kashi na biyar cikin jerin kasidun da muke kawowa kan hanyoyin da yan dandatsa ke bi wajen aiwatar da ta’addancinsu ga kwamfutocin jama’a.

A sha karatu lafiya. Darasi Na (02): “Scanning Networks” Bayan darasi kan yadda ake tattaro bayanai kan kwamfuta ko kamfani ko wata na’urar da ake son isa gare ta. A darasi na biyu mai take: “Scanning Networks,” ana karantar da dalibai ne yadda zasu yi amfani da bayanan da suka samo daga wancan bincike, wajen isa ga wata kwamfuta ko na’ura ta musamman da suka samo adireshi ko sunanta. Kafin nan, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, duk wata kwamfuta da kake iya isa gareta a tsarin sadarwa na zamani, tana ajiye ne a wani zangon sadarwa na musamman, dake wani wuri na musamman, a wata kasa ko jiha ko gari na musamman, cikin ginin wani kamfani ko ofishi ko gida ko daki na musamman. Wannan zango shi ake kira: “Local Area Network” (LAN), wanda munyi darasi kan shi a kasidarmu mai take: “Tsarin Sadarwa Tsakanin Kwamfutoci,” a shekarun baya. Wannan zango mai suna LAN a gajarce, yana dauke ne da kwamfutoci da aka hada alaka a tsakaninsu. Misali, hokumomin gwamnati da wasu kamfanoni masu zaman kansu suna da kwamfutoci da suke amfani dasu a ma’aikatansu. Wadannan kwamfutoci an hada su da juna ne, ta yadda za ka iya isa wata kwamfutar daga kwamfutar da kake aiki a kai, muddin an baka iznin yin hakan. Daga cikin wadannan kwamfutoci, duk kwamfutar dake jone da Intanet, a matsayin Uwar Garke (Web Server), idan aka gudanar da bincike mai kyau ana iya samun lambarta, wato: “IP Address”. Idan anyi sa’a ma har da sunanta (Host Name), da sunayen ma’aikatan dake hukumar (Username), da lambobin wasu kwamfutocin dake zangon baki daya. Wanda shi ne tsarin da darasin baya ke karantarwa. Da zarar ka iya samun wadannan bayanai, sai matakin tantance kwamfutocin ta hanyar bayanan da ka samu a matakin farko. Wannan shi ake kira: “Scanning Networks.” Manufa da Tsari Babbar manufar wannan mataki shi ne: “Tantance kwamfutoci da na’urorin sadarwar dake wani zango na sadarwa, don tabbatar da masu rai daga cikinsu, da abubuwan da suke dauke dasu.” A wannan mataki dai za a karantar da dalibi ne yadda zai kwankwasa kofar wani zangon sadarwa, don sanin wadanda ke cikin zangon, da bayanan da suke dauke dasu, don sanin hanyar da zai bi don daukowa ko nadewa ko saukar da duk abin da yake bukata. Hakan na yiwuwa ne ta hanyar shigar da lambar kwamfutar (IP Address, misali: 192.168.115.12) a kan wata manhaja ta musamman da aka tanada, don nemo bayanan da suka shafeta. Daga cikin bayanan kuwa akwai nau’in babbar manhaja (Operating System), da zubinta (Version), da kafofin sadarwar da kwamfutar ke dauke dasu, wato: “Ports” da manhajojin sadarwar dake dauke a kowace kafar sadarwa. Misali, a kafar sadarwa mai lamba ta: 25 ne ake samun manhajar sadarwar Imel, wato: “Simple Mail Transfer Protocol” (SMTP). A kafar sadarwa mai lamba ta 80 kuma ake samun manhajar ka’idar sadarwa ta Intanet, wadda da it ace kwamfuta ke iya sadar da keg a Intanet, wato: “Hypertext Transfer Protocol” (HTTP). Bayan haka, ta wannan hanya ne za a sanar da dalibi yadda zai gane ko wadancan kafafe na sadarwa a kunne suke ko a kashe suke. Sannan ta haka zai iya gane wasu manhajoji ne a kunne a kafar. Wadannan kananan manhajoji su ake kira: “Services.” Sannan idan kafafen a toshe suke, akwai yadda za ka iya gane dabarun da aka yi amfani dasu wajen toshe su. Sannan idan zangon sadarwa na dauke da wasu manhajojin tsaro da aka sa, irin su: “Intrusion Detection System” (IDS), ko “Intrusion Prevention Sysmte” (IPS), ko “Firewall” (Garkuwar wuta), duk za ka iya ganewa. A karshe kuma a koya maka yadda za ka iya waske wadannan hanyoyin tsaro cikin sauki. Nau’ukan Hanyoyin Tantancewa Tsarin haka alaka tsakanin kwamfutoci ya kasu kashi biyu ne: akwai tsari na kai tsaye wanda ke amfani da lambar IP. Wannan shi ake kira: “IP/TCP Connection.” Wannan tsarin ya fi aminci, wajen tabbatar da samuwar alaka tsakanin kwamfutoci wajen aika sakonni a tsakaninsu. Komai a bayyane yake. Tsari na biyu shi ake kira: “UDP Connection.” A wannan tsari, wanda yana amfani ne da tsarin wayar-iska (wato: “Connectionless system”), ba ka iya gane isar sakonni tsakanin kwamfutoci, sun isa ko basu isa ba? A tsarin farko, idan ka aika sako zuwa ga wata kwamfuta, idan a kashe take, nan take za a dawo maka da sakonka, kai tsaye. Amma a tsari na biyu, muddin sakon bai je ba, sai dai kaji shiru.

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...