Skip to main content

Posts

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1) KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya. Mabudin Kunnuwa Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi. A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka ...

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

YADDA AKE TRANSFER CREDIT A MTN

YADDA AKE TURA KUDI A LAYIN MTN WATO CREDIT TRANSFER... Idan kanason ka tura kudi daga layinka na MTN zuwa layin wani, Kawai saikaje gurinda ake rubuta sako a wayarka. Ka rubuta; Transfer saika bada yar tazara saika rubuta lambar wamda zaka turawa saika kara bada tazara sai ka rubuta adadin kudin da zaka tura saika kara bada yartazara sai ka rubuta PIN dinka saka tura zuwa 777 idan ka tura zasu bukaci ka tura kalmar YES itama zuwa 777 shikenan. Misali kanason tura Naira100 zuwa 07036413851 To kawai saikaje wajen rubuta sakoa ka rubuta; Transfer 07036413851 100 0000 saika aika zuwa 777 *600*07036413851*100*0000# 0000 nan da ka gani shine PIN number ka kuma dolene ka canja shi daga 0000 kafin kayi transfer zuwa wasu lambobin guda hudu da kaikadaine ka sansu Ga yadda ake canjawar kaje wajen rubuta sako ka rubuta 0000 saika bad tazara ka rubuta lambobi hudu da kakeso su zama sababbin PIN dinka saika kara bada tazara ka sake rubuta sababbin PIN din, Misali ace 1234 ne kakeso a matsayin s...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...

Yadda zak Goge ko Dakatar Da Facebook Ɗinka

Yadda za a goge asusun Facebook na dindindin a cikin matakai 3 masu sauƙi James Laird | Dalian da suke Mutun tunanon share facebook account ɗinsa Sune kamar haka:- Ko dai kana damuwa da wasu sirri kanka ta yanar gizo, ko kuma kawai kana gajiya da sabuntar shigar yau da kullun daga abokai na Mu'amula, ko abokai na makaranta, waɗanda ka fahimci cewa a zahiri basu da kyaky-kyawan hali, akwai wasu dalilan da yawa, da yasa zaka so ka share asusun Facebook din ka - kuma yin hakan ba shi da wahala In sha Allahu, ba kamar yadda mitane suke tunani ba. A cikin wannan maƙalar, zamuyi bayanin yadda zaka share Facebook-mataki-mataki, gami da bayyana bambanci tsakanin 'Dakatar da asusun', da kuma goge shi gaba daya. Idan kana tunanin share asusunka to ba kai bane farau. Hakan na faruwane sakamakon ɓacin rai game da tasirin matsalolin kafofin watsa labarun da ke shafar lafiyar mutum da rayuwarmu, da yawa mutane sukan ci gaba da juya baya ga waɗannan rukunin yanar gizon da suk...

YADDA AKE WANKAN GAWA

TUNATARWA WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA FALALAR WANKAN GAWA Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’ A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace: ”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin). SHARUDDAN WANKAN GAWA: Daga cikin sharaddan wankan gawa sune: {1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali: Iyaye. kanne ko yayyek “ya”yansa da sauransu). {2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta). {3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi. YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali: Sau Uku (3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9). Hakan ya tabbata daga Manzon Al...

ƘUNGIYAR MANOMA TAYI MAGANA

MANOMA: DAGA YANZU BUHUN SHINKAFA BA ZAIWUCE 15,000 BA. By: Muhammadu Auwal Umar A korarin karfafa wa gwamnatin tarayya na hana fasakaurin shinkafa a kasar nan, kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya ta ce, daga yanzu buhun shinkafa ba zai wuce naira 15,000 ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamin a garin Abuja, shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIPAN), Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya. Ya kara da cewa, shinkafar gida da ake yi a Nijeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000. Kungiyar ta bayyana cewa, ta rubuta wa gwamnatin tarayya wasika wajen karya farashin shinkafa, domin ta karfafa wa gwamnati wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan. Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Nijeriya tana asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin. Alhaji Moha...