Skip to main content

Posts

Kayan Aikin Gina Manhajar Kwamfuta Kashi na1

Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta (1) A Kashi na bakwai cikin binciken da muke yi kan tsarin gina manhajar kwamfuta. A sha karatu lafiya. Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta Kafin aiwatar da kowane irin aiki, Magina manhajar kwamfuta na bukatar kayan aiki. Wadannan kayayyakin aiki suna da yawa, dangane da girma ko mahimmancin manhajar da ake son ginawa. A tare da haka, akwai wadanda suke wajibi ne, akwai kuma wadanda samuwarsu abin so ne, ba wajibi ba. Ga wasu daga cikin kayayyakin aikinsu nan: Ilimi da Kwarewa: Wannan shi ne abu na farko. Magina manhajar kwamfuta kwararru ne, wadanda suka san kan kwamfuta da rayuwarta, da lafiyarta, da makisanta. Sanayya a wannan mahanga abin so ne wajen gina manhajar kwamfuta. Wannan ilimi kuwa ya hada da kwarewa a fagen dabarun gina manhajar da ake son amfani da shi. Ba dole bane sai ka san dukkan dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages), a a. Misali, kana iya gina manhajar kwamfuta da na wayar salula ta amfani da...

Mu'ujizar Alqu'ani Mai Girma

Gaskiyar Yadda Akeyin Ruqiya, A Musulinci Gaskiyar yadda akeyin Ruqiya, A Musulunci Watch and Understand youtube HD

New Video

youtube HD

Addu'o'i Managarta Masu Albarka

Adu'o'i Masu Fa'ida Da Albarka, من الكتاب الحسن المسلم Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Shiga Bandaki. (بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ. (Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith Addu'ar Fita Daga Bandaki. غُفْرَانَكَ. Ghufranak. Ya Allah! Gafararka (na ke nema) Zikiri yayin fara Alwala. بِسْمِ اللهِ. Bismi l-lahi Zikiri Bayan Gama Alwala أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ. Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; k...

Halifofin Shehu Ibrahim Inyass Na Nigeria

Halifofin Shehu Ibrahim Inyanss Halifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannunsa ✍️ Rayyahi Sani Khalifa Akwai wasu daga cikin halifofin Shehu a Najeriya wadanda Allah yayi musu baiwa da samun mukadamanci kai tsaye daga hannun Shehu RA, kamar yanda na samu a cikin littafin ( رجال وادوار حول صاحب الفيضة ) wanda Sheikh Muhammad dan Shehu Abdullahi Altijani ya rubuta. A cikin wannan littafin mawallafin ya tattara sunaye da takaitattun bayanai akan kowani Shehi, da kuma ainihin wasiqar/shahadar da Shehu ya rubutawa kowanni daya daga cikinsu na mukaddamanci. Wadannan shehunnai su ke da izini mudlaqi na bada darika da mukadamanci da bada izinin karanta asraran tijjaniyya ga wanda suka ga dama a kuma lokacin da suka ga dama daga wajen Shehu RTA. Wadannan dai sune tushen Faidha a Najeriya dan haka muridai da sauran al'umma ku sani cewa duk wani abu da ake danganta shi da faidha idan bai fito daga wadannan zawiyoyin ba ko rasan da su...

Yadda Zaka Samu Space A wayarka, Bayan Tacika

YADDA ZAKA SAMU 'MORE SPACE' AWAYARKA TA ANDROID, BAYAN TA CUSHE Assalamu Alaikum yaa Ƴan uwana Maza da Mata ma'abota bibiyarmu awannan Shafi mai Albarka. A yau made, da ikon Allah mun zomuku da wata tsarabar wadda zata amfane ku wajen magance matsalar da take addabar ku Awayoyinku, na ƙaraci Space. Yayi dai dai ASHA KARATU LAFIYA..... Kamar yadda kuka sanine sau da yawa mutun zaga bashi da wani Abu (files, images, apps, videos, music, e.t.c) da yawa akan wayarka amma kanaso ka Sauko da wani abu ko Atura maka, kawai sai wayar tace maka (is not enough space delet some), to In sha Allahu nesa tazo kusa. Kawai matakin farko da zakabi har ƙarshe shine:- 1. Ka shiga menu na wayarka. 2. Sai file manager 3. Danna internal memory 4. Shiga Home 5. Zaɓi ko shiga memory na kan Wayar 6. Ka duba duk folders da kake da su 7. Wanda kaga akwai wani abu mai amfani, sai ka bar shi, ko kuma ka Select (zaɓi), sai ka dubu duk inda kaga ansa alamar Almakashi, saika taɓa shi, koda g...

Ganduje Da Mataimakan Gwamnoni Uku Sun Tsalake Rijiya Da Baya

An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna legit.ng Jul 29, 2019 5:49 AM Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya ga ta kansa yayin da rikici ya kaure a filin wasan kwallon kafa ta Ahmadu Bello dake garin Kaduna, ABS, inda har sai da Yansanda suka dinga harba barkonon tsohuwa a cikin jama’a. Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli bayan an kammala wasan karshe na gasar AITEO Cup tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes. Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasan ya kai ga bugun daga kai sai gola sakamakon kunnen doki da aka tashi, daga karshe Kano Pillars ta samu nasara da ci 4-3, sai dai magoya bayan Pillars sun shiga fili a guje don murna, inda jami’an tsaro suka taresu, daga nan fa sai rikici ya kaure, shine dalilin da yasa Yansanda suka shiga harba barkonon tsohuwa. Daga cikin wadanda rikicin ya rutsa dasu akwai gwamnan jahar Kano da ya je goy aba Pilla...