Skip to main content

KIMIYAR LANTARKI A SAUWAKE (1)

Kimiyar Lantarki A Sawwake (1)

KIMIYYALANTARKI By Baban Sadik


A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya.

Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya.

Mabudin Kunnuwa

Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne. Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi.

A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne. Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa ne ta Imel. Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka sannan zan hada da sakonnin masu neman kasidu in buga.

Don haka, duk mai neman wata kasida ta musamman, yana iya aiko da bukatarsa ta adireshinmu na Imel. Akwai wadanda suka aiko da sakon bukata ta tes, ba tare da adireshin Imel ba.

Zai yi wahala a wannan yanayi in iya aika maka kasida wadda mafi karancinta shafi uku ne, ta hanyar tes a wayar salula. Dole sai ta Imel. Sai a kiyaye.

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da maudu’i na musamman kan fannin kimiyyar lantarki; wani fannin da bamu taba yin bincike a cikinsa ba, duk da mahimmancinsa ga rayuwar al’umma da tattalin arzikinsu. Rubutu kan wannan fanni na lantarki zai dauke mu wasu makonni nan gaba.

A yau zamu yi bayani ne kan mahimmancin wannan fanni, bayan takaitaccen bayani daga asalinsa. Sannan muyi bayani kan madaukan lantarki; ma’ana: mahallin da lantarki ke gudanuwa kenan.

A gaba mu kawo bayanai kan nau’ukan sinadaran lantarki. Sai kuma bayani kan yadda sinadarin maganadisun lantarki ke gudana a mahallinsa.

Daga cikin bincikenmu har wa yau, mai karatu zai ci karo da bayani kan farantin makamashin lantarki, wanda a harshen Turanci ake kira: “Electrical Circuit.” Wannan faranti shi ne hakikanin abin da idan ka fahimce shi a ilimin lantarki, ka kusan kure fannin. Domin duk wata na’urar dake dauke da sinadarai ko makamashin lantarki a wannan zamani, tana dauke ne da wannan faranti. Kada in cika ku. Daga cikin bincikenmu za mu kawo bayanai kan abubuwan da ake sarrafa su don samar da wutar lantarki a duniyar yau. Wannan zai zo ne bayan ‘yar takaitacciyar karatun tarihi da za mu yi kan asalin lantarki na zamanin da; tsakanin wanda ke samuwa daga sararin samaniya da wanda ke samuwa daga halittun dake rayuwa a teku. Za mu ci karo har wa yau da bayani kan tarihin lantarkin zamani; su wa da wa suka assasa wannan fanni a duniyar yau? Kasidar ba za ta kare ba sai masu karatu sun san yadda ake kididdige kima da yawan wuta ko makamashin lantarki dake gudanuwa a na’urorin sadarwa na zamani masu amfani da wutar lantarki. Wannan zai kaimu ga bayani kan ka’idojin ilimin kimiyya da wasu masana suka assasa don karantawa da nazarin wannan fanni a kimiyyance (Scientific Laws), irin su Ohm, da Fradays’ Laws. A karshe, masu karatu za su samu bayanai kan asalin kwan lantarki ko kayayyakin da ake amfani dasu wajen haska wutar lantarki a dakuna da gidaje da ma’aikatu ko masana’antu. Su waye suka samar dasu a asali? Wadannan, a takaice su ne kadan daga cikin abubuwan da wannan maudu’i namu zai kunsa in Allah ya so. A daya bangaren kuma, bazan yi magana a kan matsalolin wutar lantarki a Najeriya ba. Don haka, kada a rubuto mini tambaya kan wannan maudu’i. Kasidar za ta mayar da hankali ne kan fannin a ilimance, da nazarce. Manufar hakan kuwa ita ce ne don yada ilimi, ba muhawara cikin siyasar samar da wutar lantarki ba a Najeriya. Da fatan za a kiyaye wajen aiko tambayoyi ko tsokaci.

Comments

Popular posts from this blog

KIMIYAR ALQUR'ANI DA ZAMANI A INA AKA HAƊU (1)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (1) KIMIYYAR KUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Mun samu tambaya daga daya daga cikin masu karatu, wanda yake son sanin alakar dake tsakanin fahimtar malaman kimiyya na zamani kan abubuwan da suka shafi kimiyya, da kuma bayanin wasu abubuwa na kimiyya da Al-Kur’ani mai girma yayi. Shin, a ina suka hadu kuma a ina suka rabu? Wannan shi ne abin da zamu fara rubutu a kai daga wannan mako illa maa sha Allahu. A sha karatu lafiya. Tambaya “Abban Sadik, an ce masana Kimiyya na zamani sun tabbatar da wasu daga cikin Kimiyyar Al-Kur’ani mai girma. Wadanne ne daga ciki?” – Khaleel Nasir Kuriya, Kiru, Kano (GZG274): 07069191677 Gabatarwa Malam Khaleel Nasir muna godiya kwarai da wannan tambaya mai matukar muhimmanci, kuma Allah saka da alheri. Amsa wannan tambaya gaba dayanta na bukatar bincike na tsawon zamani mai dauke da hujjoji daga Kur’ani da kuma manyan littafan zamani. Domin harka ce da ta kumshi ilimi. Amma za mu yi iya kok...

Kimiyar Alqur'ani Da Zamani Part(2)

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2) KIMIYYAKUR'ANI DA ZAMANI By Baban Sadik Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya. HALITTAR DUNIYA ——————————————— Binciken Kimiyyar Zamani Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule. Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a Turance. Sai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenan. Hakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass. Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ci...