Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta (1) A Kashi na bakwai cikin binciken da muke yi kan tsarin gina manhajar kwamfuta. A sha karatu lafiya. Kayan Aikin Magina Manhajar Kwamfuta Kafin aiwatar da kowane irin aiki, Magina manhajar kwamfuta na bukatar kayan aiki. Wadannan kayayyakin aiki suna da yawa, dangane da girma ko mahimmancin manhajar da ake son ginawa. A tare da haka, akwai wadanda suke wajibi ne, akwai kuma wadanda samuwarsu abin so ne, ba wajibi ba. Ga wasu daga cikin kayayyakin aikinsu nan: Ilimi da Kwarewa: Wannan shi ne abu na farko. Magina manhajar kwamfuta kwararru ne, wadanda suka san kan kwamfuta da rayuwarta, da lafiyarta, da makisanta. Sanayya a wannan mahanga abin so ne wajen gina manhajar kwamfuta. Wannan ilimi kuwa ya hada da kwarewa a fagen dabarun gina manhajar da ake son amfani da shi. Ba dole bane sai ka san dukkan dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages), a a. Misali, kana iya gina manhajar kwamfuta da na wayar salula ta amfani da...
UMDATUL AHKAM باب الحيـــض: 40- عن عائشة رضي الله عنها "أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سألت النبي صلى الله عليه وسلم، فَقَالت: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فقالَ: لاَ، إِنَّ ذَلِكَ دَمُ عِرْقٍ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ اْلأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلَّى". وفي رواية: "وَلَيْسَتْ بِالْحَيْضَةِ، فَإِذَا أَقْبَلَتِ الْحَيْضَةُ فَاتْرُكِي الصَّلاَةَ فِيهَا، فَإِذَا ذَهَبَ قَدْرُهَا فَاغْسِلِي عَنْكِ الدَّمَ وَصَلِّي". BABUN DA ZAI YI BAYANI A GAME DA HUKUNCIN JININ HAILA: 40- An karvo daga (Nana) Aishatu (R.A) tace haqiqa Faximatu xiyar Abi Hubaishin ta tambayi annabin Allah (S.A.W.) sai tace (da shi): (Ya ma'aikin Allah) ni mace ce da nake yawan zubar jinin haila bani da tsarki shin ko na bar yin sallah? Sai ma'aiki (S.A.W.) yace da ita a'a, (ai ba kya bari ba) domin ai shi wannan wani jinin da yake zubowane daga wata jijiya (dake jikin mahaifa), sai dai ke abin da ya wajaba kiy...